Wata ƙungiya mai suna 'Arewa Youth Ambassadors (AYA)' ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da kuma hukumomin tsaro da su gaggauta sakin She...
Wata ƙungiya mai suna 'Arewa Youth Ambassadors (AYA)' ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da kuma hukumomin tsaro da su gaggauta sakin Shehu Musa Aljan, wani jarumi daga Arewa da ya shahara wajen taimaka wa jami’an tsaro yaƙi da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu miyagun laifuka a yankunan Arewa.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin, wacce Kwamred Yahaya M. Abdullahi ya sanya wa hannu, AYA ta bayyana matuƙar damuwar ta kan ci gaba da tsare Aljan da kuma yanke masa hukuncin shekaru 45 a gidan yari, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma da manyan shugabanni a yankin Arewa, musamman waɗanda suka san irin gudumawar da ya ke bayarwa a harkar tsaro.
AYA ta bayyana cewa Shehu Musa Aljan ya shafe shekaru yana aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro.
Ƙungiyar ta jaddada cewa duk da haɗarin da yake fuskanta, Aljan ya taka rawar gani wajen tarwatsa ƙungiyoyin ta’addanci da dawo da zaman lafiya a yankuna masu fama da tashin hankali.
A watan Disamba 2019, rahoton AYA ya nuna cewa Aljan ya bi sawun wasu ’yan bindiga a hanyar Abuja–Kaduna, inda ya kama wasu daga cikinsu tare da ceto shanu sama da 1,000 da aka sace a yankin Rijana.
Haka kuma ya ƙwato makamai ciki har da, Bindigogin AK-47, AK-49, da Sauran bindigogi da dama, da kuma Dubunnan harsasai
Rahoton ya kara da cewa ’yan bindigar sun yi ƙoƙarin ba shi Naira Miliyan 2 domin ya barsu su tsallaka gadar Kaduna da shanun, amma ya ƙi amincewa.
Aljan ya sha bayyana adawarsa da tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai cewa ba abin yarda ba ne domin ba su da gaskiya ko mutunci
AYA ta ce bayan wani aiki da Aljan ya yi na taimakawa jami’an tsaro wajen kama wasu ’yan bindiga a Jihar Bauchi, lamari ya sauya ba zato ba tsammani.
An kama shi, an gurfanar da shi, daga ƙarshe kuma aka yanke masa hukuncin shekaru 45 a gidan yari.
Ƙungiyar ta tabbatar da cewa bayan gudanar da nata bincike, shugabannin al’umma da dama sun tabbatar da cewa Aljan ya miƙa duk waɗanda ya kama da makamansu ga jami’an tsaro kamar yadda ya saba.
Sai dai daga baya, wanda ke taimaka wa al’umma ya zama wanda ake zargi.
AYA ta bayyana cewa wannan lamari ya tayar da hankalin al’umma, domin mutum irin Aljan da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare jama’a yanzu yana shan wahala a gidan yari.
A cewar ƙungiyar “’Yan bindiga suna jin tsoron a kira sunan Aljan, ba don yana tattaunawa da su ba, sai don yana fafatawa da su yana kama su.”
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnati da ta, Gaggauta sakin Musa Nura Aljan ba tare da sharadi ba tare da Gudanar da bincike na gaskiya da na bainar jama’a kan shari’arsa
AYA ta yi gargadi cewa Najeriya ba za ta samu ci gaba ba matuƙar ana gallaza wa mutanen da ke kare al’umma.
“Arewa ba za ta yi shiru ba yayin da ɗanta jarumi yake shan wahala a gidan yari. Kujerun mulki na wucewa ne, amma adalci da gaskiya ba sa shuɗewa.”
Ƙungiyar ta jaddada aniyarta na ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya, adalci, da kare duk masu bada gudummawa wajen tsaron ƙasa.

No comments