Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗalibai Mata Na Kebbi da Aka Sace Sun Kuɓuta

Ɗalibai mata da aka sace daga wata makaranta a jihar Kebbi sun samu ‘yanci, lamarin da ya kawo ƙarshen fargaba da damuwar da iyalai da al’um...




Ɗalibai mata da aka sace daga wata makaranta a jihar Kebbi sun samu ‘yanci, lamarin da ya kawo ƙarshen fargaba da damuwar da iyalai da al’umma ke ciki tun hare-haren da aka kai makarantar ranar 17 ga Nuwamba.

Wata majiyar tsaro da ta sanar ta bayyana cewa an kubutar da ɗaliban ne da safiyar Talata, bayan haɗaɗɗun matakan da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA) da Hukumar Tsaro ta DSS suka ɗauka. Sai dai majiyar ba ta bayar da cikakkun bayanai ba, amma ta tura hotunan ɗaliban da aka ceto.

An kai harin ne a Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke Maga, inda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da ɗalibai 25, suka kuma kashe mataimakin shugaban makarantar a lokacin harin. Daga baya ɗaya daga cikin ɗaliban ta tsere.

A halin yanzu, hukumomi ba su fitar da cikakken bayani game da yadda aka kubutar da su ba, yayin da ake sa ran ƙarin rahoto zai biyo baya.

No comments