Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hedikwatar Tsaro Ta Fara Binciken Batun Janye Sojoji Mintuna Kafin Sace Ɗalibai A Kebbi

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce ta fara bincike kan zargin da ake yi cewa an janye jami’an tsaro kimanin rabin sa’a kafin ’yan bindig...




Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce ta fara bincike kan zargin da ake yi cewa an janye jami’an tsaro kimanin rabin sa’a kafin ’yan bindiga su kai harin da ya kai ga sace ɗalibai mata na Sakandaren Gwamnati da ke Maga, ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

A ranar 17 ga Nuwamba ne ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar tare da yin garkuwa da dalibai 25.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar daga Abuja a ranar Lahadi, yana mai cewa sun karɓi maganganun Gwamnan Kebbi da ke cewa ’yan ta’adda sun kai hari bayan mintuna 30 da janye sojoji daga yankin.

DHQ ta ce ana gudanar da zurfin bincike kan yadda aka yi da batun tura sojoji da janyensu a lokacin harin, domin gano ainihin gaskiya kan al’amuran da suka faru.

Onoja ya ce duk wani kuskure da aka gano zai fuskanci gyara cikin gaggawa, domin an fi dogaro da bayanan leƙen asiri wajen yanke matakan tsaro a yankunan da ake fama da hare-hare.

Ya ƙara da cewa, sojoji na bi sahun duk wata sahihiyar bayanan sirri domin ganin an ceto daliban da aka sace, tare da yin aiki kafa-da-kafa da gwamnatin jihohi, shugabannin al’umma da sauran hukumomin tsaro wajen ƙara tsaurara tsaro a makarantun yankuna masu rauni.

DHQ ta nuna damuwa matuƙa kan harin da ya faru a Kebbi da kuma wanda ya afku a St. Mary’s Catholic School Papiri da ke Agwara, jihar Neja, wanda shima ya shafi sace ɗalibai.
Onoja ya bayyana wadannan hare-hare a matsayin “ayyukan ta’addanci marasa imani”, yana mai tabbatar da cewa dakarun ƙasa na ci gaba da gudanar da aiki ba tare da hutawa ba wajen farfado da zaman lafiya da kubutar da wadanda aka sace.

A cewarsa, rundunar soji tana lura da damuwar jama’a kan ƙarin tashin hankalin da ake fuskanta a arewacin ƙasar kwanan nan, tana mai sake jaddada cewa rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da kare rayuka a dukkan yankunan da abin ya shafa.

No comments