Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta A Neja, Sun Yi Awon Gaba Da Ɗalibai Da Malamai

Rahotanni daga Jihar Neja sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kutsa makarantar firamare da sakandare ta St. Mary da ke Papiri, a ƙaramar h...




Rahotanni daga Jihar Neja sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kutsa makarantar firamare da sakandare ta St. Mary da ke Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama a wani hari da aka kai da daren Alhamis.

Wata majiya ta ce maharan — waɗanda yawansu ya kai a kan babura kusan 60 tare da wata mota — sun iso cikin dare, suka bude wuta, lamarin da ya jikkata mai gadin makarantar kuma aka bar shi cikin munanan raunuka.

“Lamarin ya faru tsakanin ƙarfe uku zuwa hudu na asuba. Ba a tantance yawon yaran da aka sace ba tukuna,” inji wani mazaunin Agwara da ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Wasu kuma sun ce maharan ba kawai ɗalibai suka tafi da su ba, har da wasu malamai da suke tsaka da bacci a makarantar.

“Malamai da ɗalibai an fizge su da karfi a cikin dare. Wannan wani mummunan lokaci ne ga iyalai da al’ummomin yankin baki ɗaya. Yaran nan marasa laifi ne, kuma malamansu masu sadaukarwa ne — rayukansu yanzu na cikin hadari,” inji wata majiya a yankin.

Duk da cewa ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba, wasu mazauna yankin sun ce yawan na iya wuce mutane 100.

Rundunar ’yan sandan jihar Niger ta tabbatar da harin a wata sanarwa da kakakinta, SP Wasiu Abiodun, ya fitar. Ya ce an tura jami’an taktik da sojoji da sauran jami’an tsaro domin shiga dazukan da ke kewaye da yankin don neman yaran cikin gaggawa.

Kwamishinan ’yan sanda, CP Adamu Elleman, ya bayyana cewa ana gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, tare da gargadin cewa gwamnati za ta ɗauki mataki a kan hukumar makarantar saboda ta ci gaba da gudanar da karatu duk da gargadin gwamnati cewa a rufe makarantun yankin sakamakon barazanar tsaro.

Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu tare da ba jami’an tsaro bayanai masu amfani domin taimakawa ceto ɗaliban cikin hanzari.

No comments