Gwamnatin Tarayya ta ƙara tsaurara matakai kan batun sace ɗalibai mata sama da 20 da ’yan bindiga suka yi wa ƙauyen Maga a ƙaramar hukumar D...
Gwamnatin Tarayya ta ƙara tsaurara matakai kan batun sace ɗalibai mata sama da 20 da ’yan bindiga suka yi wa ƙauyen Maga a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, da ya tashi nan take zuwa jihar don shiga tsakani kai-tsaye.
Wannan mataki na shugaban ƙasa ya zo ne a lokacin da ake ƙara matsa wa gwamnati lamba daga sassa daban-daban na ƙasar domin ganin an ceto yaran cikin gaggawa.
Abdulaziz Abdulaziz, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, ya shaida cewa Minista Matawalle zai yi aiki kafa ɗaya da jami’an tsaro da ke kan aikin ceto a yanzu haka.
A cewarsa, da zarar ministan ya isa Kebbi, zai haɗa kai da hukumomin tsaro na ƙasa da na jihar Kebbi domin jagorantar sabon salo na bincike da sintiri. Ya ƙara da cewa, Minista Matawalle na zuwa da takamaiman kwarewa wadda ke da muhimmanci a irin wannan yanayi.
Abdulaziz ya tunatar da irin rawar da Matawalle ya taka lokacin da yake gwamna a Zamfara, lokacin da aka sace ɗaliban makarantar Kankara kusan 300 a makwabciyar jihar Katsina. Ya ce gogewarsa wajen shiga tattaunawa da gudanar da dabarun tsaro a irin wannan lokaci na daga cikin dalilan da suka sa Shugaba Tinubu ya zaɓe shi don ya jagoranci wannan aiki.
A ranar Litinin 17 ga Nuwamba ne maharan suka kutsa cikin makarantar da asuba, lokacin da ɗaliban ke shirin fita sallar asuba. Rahotanni sun ce sun kashe mai gadi sannan suka yi awon gaba da ’yan matan bayan sun ci gaba da harbi mai yawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasagu, Hon. Hussaini Aliyu Bena, ya bayyana cewa maharan ba su zo da babura ko motoci ba kamar yadda suke saba, sai dai sun nufo makarantar a ƙafa, abin da ya sa harin ya zo musu a bazata.
Yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da fatattakar ’yan bindigar a dazukan yankin, yayin da gwamnati ke nanata cewa tana daukar dukkan matakan da suka dace domin ganin yaran sun koma hannun iyayensu lafiya.
.jpg)
No comments