Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PASAN Ta Kulle Majalisar Dokokin Bauchi Kan Cin Gashin Kan Majalisu, Ta Tsunduma Yajin Aiki

Daga Khalid Idris Doya  Ƙungiyar Ma'aikatan Majalisar Dokoki Ta Ƙasa 'Parliamentary Staff Association of Nigeria' (PASAN), reshe...


Daga Khalid Idris Doya 

Ƙungiyar Ma'aikatan Majalisar Dokoki Ta Ƙasa 'Parliamentary Staff Association of Nigeria' (PASAN), reshen jihar Bauchi ta tsunduma yajin aikin sai baaba-ta-gani domin matsa ƙaimi wajen ganin buƙatarta na cin gashin kan majalisun dokoki na jihohi a ɓangaren hidimar kuɗi ya samu tabbatuwa.

Da ya ke ganawa da 'yan jarida a ranar Juma'a, shugaban PASAN reshen jihar Bauchi, Kwamared Adamu Yusuf, ya ce, wannan matakin ya biyo bayan umarnin da suka samu ne daga uwar ƙungiyar na ƙasa. 

Ya ce mambobin ƙungiyar ba su da wani zaɓi ne illa su rufe dukkanin ayyukan majalisar dokokin jihar Bauchi har sai an cika musu buƙatunsu.

A cewarsa, sun tafi yajin aikin ne domin matsa lamba wa gwamanti da ta aiwatar da cin gashin kan majalisun dokokin na jihohi, inda ya misalta matakin a matsayin abu mai muhimmanci wajen inganta ayyukan majalisjn dokokin jihohi cikin gaskiya a faɗin ƙasar nan. 

Ya ƙara da cewa cin gashin kan majalisu zai kuma bada dama wajen ƙara inganta mulkin demokraɗiyya da kyautata ayyuka.

Kwamared Yusuf ya bayyana cewar ƙungiyar PASAN ta gudanar da yajin aikin gargaɗi da daman gaske a baya kan ganin an aiwatar da dokar cin gashin kan majalisun dokoki, amma har yanzu gwamnatin tarayya na ci gaba da jan ƙafa wajen aiwatar da dokar.

Ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su ci gaba da mara wa yunƙurin ƙungiyar baya, ya tabbatar da cewa tsawon lokaci ƙungiyar ta gama ƙure haƙurinta domin ta shiga tattaunawa da ganawa da hukumomin gwamnati sau da dama amma haƙa ba ta cimma ruwa ba. 

Duk da matakin yajin aikin, Yusuf ya jinjina wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a bisa ƙoƙarinsa na ganin majalisar dokokin jihar ta samu cin gashin kanta. Ya ce, ƙoƙarin Gwamnan na taimakawa wajen inganta mulkin demokraɗiyya.


 

No comments