Daga Khalid Idris Doya Gwamnan jihar Gombe Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya raba sabbin motoci 16 ga Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara da Khadi-Kh...
Daga Khalid Idris Doya
Gwamnan jihar Gombe Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya raba sabbin motoci 16 ga Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara da Khadi-Khadi na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a, da nufin ƙara inganta harƙar shari’a, da sauƙaƙa musu zirga-zirga gami da kuma cin gashin kan sashin.
Motocin da gwaman ya rabar sun haɗa da ƙirar 2025 model Toyota SUVs guda biyu wa Babban Alkalin Alkalan jihar da kuma Grand Khadi, sai kuma wasu sabbin motocin na zamani ƙirar 2025 model GAC SUVs guda 14 da aka ranar wa Alkalan manyan kotuna da Khadi-Khadi na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a.
Da ya ke miƙa motocin a ranar Juma'a gwamna Inuwa wanda mataimakinsa Dakta Mannasah Daniel Jatau ya wakilta, ya ce wannan karimcin na nuna himmatuwar gwamnati wajen samar da muhimman kayan aiki na samar da ingantacciyar hidima daga dukkanin rukunan gwamnati.
Ya ƙara da cewa samar da motocin ya yi daidai da ƙudurin gwamnan na gina daidaitaccen tsarin shari’a, da ingantattun kayan aiki da cikakken ‘yancin cin gashin kai wanda zai samar da ayyuka masu inganci ga jama'a akan lokaci.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Inuwa tana ci gaba da tinƙarar ƙalubalen da aka daɗe ana fama da shi a dukkan ɓangarorin bisa alƙawuran da ta yi wa jama’a, ciki har da ƙoƙarin da ake yi na magance matsalolin da aka gada da kuma tabbatar da biyan albashi cikin gaggawa.
"Gwamna ya yi nasa ƙoƙari, kamar yadda kuke gani, waɗannan motoci sabbi ne 'yan yayi na 2025, don haka ina ƙira ga waɗanda suka amfana su yi amfani da su yadda ya kamata wajen gudanar da ayyukansu. Yanzu ya rage ga waɗanda suka ci gajiya su ririta wannan ƙoƙari don gudanar da ingantaccen aiki," in ji shi.
Tun da farko kwamishinan kuɗi da bunƙasa tattalin arziƙi Malam Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo sabbin motocin guda 16 ne ga dukkan alkalai da khadi-khadi da babbar Alkaliya da kuma Babban Khadi, akan kuɗi fiye da naira biliyan biyu.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, wannan shi ne karon farko cikin fiye da shekaru goma da sashin na shari’a ke samun sabbin motocin aiki, yana mai bayyana matakin a matsayin wani babban ci gaba ga ‘yancin cin gashin kan shari’a.
A nasa jawabin, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati Barrister Zubairu Muhammad Umar, ya bayyana hakan a matsayin cika alƙawarin da aka daɗe ana yi na sake fasalin ɓangaren shari’a.
Ya yi nuni da yadda ake ci gaba da gina katafariyar babbar kotun zamani na fiye da Naira biliyan 16 a matsayin ƙarin shaida na jajircewar gwamnatin.
Ya bayyana cewa jami’an shari’a da dama sun kwashe fiye da shekaru 12 ba tare da an basu motocin aiki ba, duk da wajibcin sabunta motocin duk bayan shekaru huɗu.
Babban Lauyan ya ƙara da cewa, shekaru huɗu da suka gabata, sabbin alƙalai da khadi-khadi da aka naɗa a lokacin sun samu motocin aiki ne jimkaɗan bayan rantsar da su, inda ya ce sabon matakin ya ƙara jaddada aniyar gwamnati na sauya irin waɗannan halaye a kan kari bisa tsarin da aka gindaya na tsawon shekaru huɗu.
Shi ma da ya ke jawabi, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya Reshen Gombe Barr. Zubairu Alhassan, ya ce samar da ababen hawan ga alƙalai na nuna mutunta doka da kuma ƙudurin ƙarfafa adalci a faɗin jihar.
Da suke tsokaci a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, manyan masu gabatar da ƙara na babbar kotu da kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a sun nuna matuƙar godiya ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa irin goyon bayan da yake bai wa ɓangaren shari’a.
Sun yi nuni da cewa, samar da motocin aikin ga Alƙalai zai inganta zirga-zirgar jami’ai, da samar da aiki da kuma samar da adalci a faɗin jihar baki ɗaya.






No comments