’Yan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da ’yan mata goma sha uku a wani sabon hari da suka kai kan manoma a yankin Askira-Uba, Jihar Borno. Lama...
’Yan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da ’yan mata goma sha uku a wani sabon hari da suka kai kan manoma a yankin Askira-Uba, Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a gundumar Mussa, inda matasan mata ke aikin gona lokacin da mayakan suka iso, suka tarwatsa su, sannan suka tafi da su cikin daji.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdullahi Askira, wanda ke wakiltar Askira-Uba Constituency, ya tabbatar da sacewar a ranar Lahadi. Ya ce matasan mata da aka sace na da shekaru daga 15 zuwa 20, kuma suna aikin girbi ne lokacin da maharan suka bayyana.
Askira ya bayyana cewa waɗannan ’yan mata sun fito ne daga cikin mutanen da gwamnatin jiha ta maida su daga Huyim zuwa Mussa, domin tsira daga matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar yankin.
“Waɗanda abin ya rutsa da su na daga cikin mutanen da aka mayar da su Mussa don yin aikin gona tare da haɗin kan al’umma,” inji shi.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ’yan matan ta samu ta tsere tun da sanyin safiyar Lahadi, ta koma wajen iyalinta cikin tsira.
Sai dai har yanzu ƴan mata 12 — mafi yawansu tsakanin shekaru 15 zuwa 20 — suna hannun masu garkuwa, kuma babu masaniya kan inda aka kai su.
A nasa martanin, Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya la’anci harin, yana mai kira ga jami’an tsaro su tashi tsaye wajen ceto waɗanda ke hannun mayakan cikin lafiya.
Ya yi kira ga jama’a su ci gaba da addu’a tare da ba da bayanan da ka iya taimakawa wajen gano maboyar miyagu.
A halin yanzu, babu wata sanarwa kai tsaye daga rundunar soji ko sauran jami’an tsaro, sai dai rahotanni na cewa yan banga da masu gadin gari sun fara bincike a dazuzzukan da ke kusa.

No comments