Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babu Inda Aka Umarci Musulmi Ya Kashe Wanda Ba Musulmi Ba A Alƙur'ani – Asari

Fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon Kalabari, Asari Dokubo, ya fito fili ya ƙaryata ra’ayin cewa Alƙur’ani yana umartar Musulmai su kashe waɗa...



Fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon Kalabari, Asari Dokubo, ya fito fili ya ƙaryata ra’ayin cewa Alƙur’ani yana umartar Musulmai su kashe waɗanda ba su bi addinin Musulunci ba.

A wani faifan bidiyo da ya wallafa, Dokubo ya bayyana cewa irin waɗannan kalamai “ruɗu ne” da kuma warware fahimtar da ta dace game da addinin Musulunci.

Ya ce, Alƙur’ani ya fayyace cewa Musulmi su kare kansu idan aka kai musu hari, ba wai su fara tayar da fitina ko tashin hankali ba. A cewarsa, nassosin da ake kuskuren furtawa galibi an saukar da su ne a yanayin yaƙin kare kai, ba a matsayin izinin kai farmaki ga waɗanda ba su yi musu komai ba.

Dokubo ya ce, “Alƙur’ani ya ce: ‘Ku kai musu hari inda suka kai muku hari, kuma ku kore su inda suka kore ku.’ Wannan doka ce ta kare kai. Kowace al’umma a dokokinta tana amincewa mutum ya kare kansa. Hakika, kowa yana da hakkin rayuwa, ba wanda yake da ikon ɗaukar rayuwar wani.”

Ya ƙara da cewa ya karanta Alƙur’ani tun daga farko har ƙarshi, kuma bai sami ayar da ta umarci Musulmi su kashe wadanda ba su Musulmi ba. Haka kuma ya ce ya yi karatun Littafi Mai Tsarki ma tun daga farko har ƙarshe, domin fahimtar bambance-bambancen addinai.

Masu lura da bidiyon sun yaba da bayanin nasa, suna cewa irin wannan ƙarin haske na taimakawa wajen kawar da kuskuren fassara da ake yawan yadawa musamman a kafafen sada zumunta.

No comments