Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗalibai 50 Sun Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa A Neja

Aƙalla ɗalibai 50 daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, Jihar Neja, da aka sace a ranar Juma’a, sun tsere daga cikin daji...



Aƙalla ɗalibai 50 daga makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, Jihar Neja, da aka sace a ranar Juma’a, sun tsere daga cikin dajin da ake tsare da su, sun kuma haɗu da iyayensu lami lafiya. Sai dai fiye da 253 ɗalibai da malamai 12 har yanzu suna hannun masu garkuwa.

Shugaban CAN na Jihar Neja kuma Bishop ɗin Kontagora, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, shi ne ya tabbatar da sabon bayanin a ranar Lahadi — labari na farko mai kwarin gwiwa tun bayan sace ɗalibai sama da 300 da ya girgiza ƙasar.

A cewar Daniel Atori, mai magana da yawun Bishop Yohanna, “Mun sami labari mai daɗi domin ɗalibai 50 sun kubuta, yanzu suna tare da iyayensu. Sun tsere tsakanin Juma’a da Asabar, kuma suna ta komawa gida ne, ba makaranta ba, hakan ya tabbatar da cewa sun kuɓuta.”

A cikin bayanin an ce:

Makarantar na da 430 ɗalibai gaba ɗaya.

377 daga cikinsu ‘yan kwana ne, 53 kuma ba su kwana.

Bayan tantancewa, har yanzu ana da 141 da ba a sace su ba.

Bishop Yohanna ya roki a ci gaba da addu’a da natsuwa, yana mai cewa, “Ko da muna murna da dawowar waɗanda suka tsere, ina roƙon kowa ya ci gaba da addu’a domin a ceto sauran cikin lafiya. Mu ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro da hukumomi domin gaggauta kubuta.”

An sace ɗalibai sama da 300 ne lokacin da miyagu suka kutsa St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwarra.

A cikin sabon cikakken ƙididdigar da CAN ta fitar bayan tantancewa, an bayyana cewa:

303 ɗalibai da malamai 12 ne aka saci,

A farkon rahoto dai, an yi zaton 227 ne,

Amma daga baya an gano ƙarin 88 da aka ɗauka lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.

Bishop Yohanna ya bayyana cewa:
“Mun yi kira ga iyaye, mun sake bin diddigi, sai muka gano wasu da muka yi zaton sun tsere, ashe ma an sake cafke su. Tantancewar da muka yi ta tabbatar da hakan.”

No comments