Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: An Ceto Mutum 38 Da Aka Sace A Kwara

Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar cewa an kubutar da ’yan mutum 38 da aka sace a harin da aka kai Cocin Christ Apostolic Ch...




Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya tabbatar cewa an kubutar da ’yan mutum 38 da aka sace a harin da aka kai Cocin Christ Apostolic Church (CAC) a garin Eruku, Jihar Kwara.

An kubutar da su ne a ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba, bayan ayyukan tsaro masu tsanani da aka gudanar tare da haɗin kan hukumomin tsaro na ƙasa.

A cikin sanarwar da Kakakin Gwamna, Rafiu Ajakaye, ya fitar, Gwamnan ya danganta nasarar aikin ga abin da ya kira “tsoma bakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kai tsaye cikin lamarin” tun daga farkon rikicin har zuwa ceton mutanen.

Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya soke halartar taron G20 a Afirka ta Kudu domin mayar da hankali kan matsalolin tsaro da suka kunno kai a Kwara da Kebbi. Ya ce wannan mataki ya nuna yadda Shugaban ya sanya rayukan ’yan ƙasa a gaba.

Ya bayyana cewa umarnin Shugaban qasa na ƙara tsaro cikin gaggawa ya kawo ƙarin qungiyoyin takis na ’yan sanda hudu zuwa jihar, tare da goyon baya daga sauran hukumomin tsaro.

Gwamnan ya yaba wa hadin kan Ofishin Mai Ba Shugaban Qasa Shawara kan Tsaro, DSS, Sojojin Nijeriya, NIA, da Rundunar ’Yan Sanda bisa yadda suka gudanar da aikin cikin tsari. Haka kuma ya gode wa shugabannin al’umma, addinai da mazauna yankin bisa addu’o’i da goyon bayan da suka bayar.

Ya ce duk da cewa lamarin ya kasance abin takaici, ya qarfafa wajen inganta leqa-leqa, sa ido kan dazuzzuka da kuma inganta dabarun gaggawa don kare rayuka a jiharsa. Gwamnan ya tabbatar cewa za su ci gaba da aiki tare da Shugaba Tinubu da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Kwara.

No comments