Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaryata Rahoton Jaridar Sahara Kan Kuɗin Tsaro

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ta ƙaryata wani rahoton bogi da jaridar  Sahara Reporters ta wallafa, wanda ke iƙira...

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ta ƙaryata wani rahoton bogi da jaridar  Sahara Reporters ta wallafa, wanda ke iƙirarin cewa babu ko sisin kwabo da aka kashe a bangaren tsaro.

A cewar ma'aikatar tsaron wannan rahoto ƙarya ne kuma an wallafa shi ne da gangan domin yaudarar jama’a, tana mai cewa gwamnatin Malam Uba Sani ta daɗe tana bai wa tsaro muhimmanci ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin fasahar sa-ido, kayan aiki, motocin aiki da kuma ƙarfafa leƙen asirin al’umma waɗanda suka kai darajar biliyoyin naira.

A wata sanarwa da Kwamishinan ma'aikatar tsaron  Barista Sule Shu'aibu ( SAN) ya fitar yace daga cikin sabbin matakan tsaro da aka ɗauka akwai tura sabbin sansanonin Forward Operating Bases, motocin Hilux guda 150, da babura 500 domin karfafa yaki da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ya ce ma’aikatar ta sake tabbatar da ƙudirin Gwamna Uba Sani na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga kafafen yada labarai su rika tabbatar da sahihanci da adalci a rahotannin su.
 

No comments