Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kasafin Shekara Na 2026 Na Naira Biliyan 985.9

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma’ar nan ya gabatar da nasarorin da gwamnatin sa ta cimma tare da bayyana sabuwar taswirar...


Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma’ar nan ya gabatar da nasarorin da gwamnatin sa ta cimma tare da bayyana sabuwar taswirar ci gaba a yayin taron tattaunawa da jama’a kan kasafin kuɗi na 2026.

Gwamna Uba Sani ya sake jaddada ƙudurinsa na tafiyar da gwamnati mai adalci, daidaito, da kuma zuba jari mai ma’ana wanda zai kawo sauyi kai tsaye ga al’ummomi a fadin jihar.

A bangaren  gina Manyan Hanyoyi da Ci gaban Karkara, Gwamnan ya bayyana cewa an kammala gina tituna  sama da kilomita 785 a Mataki na 1, yayin da ake ci gaba da aikin wasu kilomita 550 a Mataki na 2 a dukkan kananan hukumomi 23.

Waɗannan ayyuka na da nufin inganta hanyoyin sadarwa, farfado da tattalin arzikin karkara, da kuma sauƙaƙa zirga-zirga a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na shirin fara aikin Jirgin Ƙasa na zamani  da samar da  motocin safa fasa na zamani (BRT), wanda zai sanya Kaduna  ta zama jiha ta biyu a Nijeriya da ta rungumi irin wannan tsarin zamani na sufuri.

A Fannin Kiwon Lafiya, Gwamna Sani ya jaddada cewa an inganta cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 200, lamarin da ya sanya Kaduna  ta zama jiha mafi kyawu a Arewa maso  Yamma da kuma ta biyu a fadin kasa wajen gudanar da harkokin kiwon lafiya a matakin farko.

Haka kuma ya bayyana ci gaban da aka samu wajen gyara tare  fadada, da samar da kayan aiki ga asibitocin gwamnati 32, inda 14 daga ciki aka kammala su. Wannan ya tabbatar da karin damar samun ingantacciyar kiwon lafiya musamman ga al’ummomi masu nisa da birane.

Hakazalika a bangaren taimaka wa Manoma da Inganta Tattalin Arziki, Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta raba motoci masu daukar kaya 900 na taki ga kananan manoma fiye da 200,000, tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar zuba jarin kaji na dala miliyan 450 da gwamnatin kasar Sin. 

Kaduna na fitowa a matsayin cibiyar koyon sana’o’i a Nijeriya, inda matasa 90,000 ke koyon kwarewa daban-daban, yayin da 32,000 suka amfana da horo na kasa da kasa.

Shi ma a nasa jawabin, Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi na jihar Kaduna Mukhtar Ahmed Monrovia, ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 80.2 a cikin kasafin 2026 domin biyan bashin da aka gada daga gwamnatoci da suka gabata.

Ya bayyana cewa duk da nauyin bashin  ciki har da na ƙasashen waje har zuwa shekarar 2026 Gwamna Sani bai ci bashin  kobo guda ba tun da ya hau mulki, yana dogaro da ingantaccen tsarin tara kudaden shiga da tsare-tsaren kashe kudi.

Ya kuma sanar da sabbin tsare-tsaren kula da kudaden gwamnati, inda ya kawo karshen tsarin da ‘yan kwangila ke neman alfarma kafin biyan su. Daga yanzu, za a biya kwangila kai tsaye bayan amincewa da takardunsu.

Kasafin Kuɗin 2026: Mai  taken Zuba Jari da Tallafa wa Jama’a:
Gwamna Sani ya gabatar da kasafin  naira biliyan 985.9  na shekarar 2026  karin kaso 24.73% daga na shekarar 2025.

Kasafin ya ware kashi 71%  naira biliyan 699.7  ga ayyukan ci gaba, yayin da kashi 29%  wato naira biliyan.2 ga kudaden gudanarwa. Muhimman sassa sun hada da:

Ilimi  kashi  (25%)

Ayyukan Gine-gine kashi  (25%)

Lafiya  kashi (15%)

Noma  kashi (11.5%)

Tsaro da Gina Zaman Lafiya  kashi (6%)

Tallafin Jama’a kashi  (5%)

Muhalli & Sauyin Yanayi  kashi (4%)

Sauran  kashi (8.5%)

Gwamnan ya jaddada matsayin Kaduna a matsayin zuciyar siyasa a  Arewacin Nijeriya. Ya mika godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zabar Kaduna a cikin masu cin gajiyar zuba jari na dala miliyan 450, kana ya yi godiya ga kasar Sin bisa goyon bayan da take bai wa jihar.

Gwamna Sani ya yi alkawarin ci gaba da hanzarta ci gaba, aiwatar da  adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa kowane dan Kaduna zai ji tasirin cigaban da ake samu yayin da jihar ke matsawa gaba cikin shekarar 2026 da ma bayan haka.



 

No comments