Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TSARO: Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Tura Sojoji A Jihar Zamfara Don Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda

Gwamnatin Tarayya ta ƙara tura ƙarin sojoji zuwa jihar Zamfara domin ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu laifi a jihar. Ƙaramin M...


Gwamnatin Tarayya ta ƙara tura ƙarin sojoji zuwa jihar Zamfara domin ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu laifi a jihar.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Gusau a ranar Juma’a.

“Ina nan tafe don haɗuwa da sojoji domin ba su umarnin da zai tabbatar da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a jihar,” in ji Matawalle.

Ya ƙara da cewa, “Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Daga yanzu, babu wanda zai ce yana jiran umarni daga sama. Mu ne za mu ba da umarni kuma za mu tabbatar an kawo ƙarshen duk wani nau’in laifi a faɗin ƙasa.”

Matawalle ya yaba wa magoya bayan APC bisa goyon bayan su ga Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC guda ɗaya a zaben 2027.

Ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin “shugaba mai hangen nesa da manufofi da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan al’umma,” inda ya kawo misalin gina babbar hanya mai layi biyu tsakanin Zaria zuwa Sokoto a matsayin shaida.

Ministan ya yi kira ga ‘yan APC da su ci gaba da wayar da kan jama’a domin samun karin goyon baya ga Tinubu a gabanin zaben gaba.
 

No comments