Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PDP Ta Kori Wike A Gaban Dubban Mutane A Ibadan

Jam’iyyar PDP ta sake shiga sabon zangon rikici a ranar Asabar, inda ta kori fitattun jiga-jiganta ciki har da Ministan Babban Birnin Tarayy...



Jam’iyyar PDP ta sake shiga sabon zangon rikici a ranar Asabar, inda ta kori fitattun jiga-jiganta ciki har da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose; da tsohon Sakatare Janar na jam’iyya, Sanata Samuel Anyanwu, a lokacin babban taronta na Ĉ™asa da aka gudanar a Ibadan.

Wannan mataki ya biyo bayan wata takun-tsaka mai zafi da ta daɗe tana ci tsakanin bangarorin jam’iyyar, musamman bangaren Wike da ya shafe kwanaki yana Ĉ™oĈ™arin dakatar da taron gaba ɗaya ta hanyar kotu.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban PDP na Kudu, Chief Olabode George, ne ya ɗaga hannun gabatar da shawarar korar su Wike a dandalin taron, sannan Hon. Samaila Burga, shugaban PDP na Bauchi, ya mara masa baya ba tare da ɓata lokaci ba. Wannan mataki ya jawo Ĉ™aruwar hayaniya da mamaki a cikin mahalarta taron, inda wasu suka ce mataki ne da zai kammala rarrabuwa a cikin jam’iyyar.

Kafin taron, mabiya Wike sun garzaya kotu suna neman a dakatar da gudanar da shi. Sai dai kotun jihar Oyo ta bai wa jam’iyyar damar ci gaba bayan ta yi watsi da bukatar dakatarwa. Amma duk da haka bangaren Wike ya ci gaba da jayayya, yana kiran taron “maras inganci” tare da cewa babu wani daraja na doka da yake da shi.

Shugaban majalisar amintattu na bangaren Wike, Mao Ohuabunwa, ya fito fili ya nesanta bangarensu daga taron, yana mai cewa NWC na su ya yanke shawarar mutunta hukumomin kotu. Ya ce duk wanda ke zuwa Ibadan ya je ne don “hutawa”, ba don halartar wani taro na jam’iyya ba. Ya kuma yi nuni da cewa Sanata Anyanwu ma ya riga ya bayar da sanarwar dage taron.

Haka ma shugaban rikon-kwarya na bangaren, Abdulrahman Muhammad, ya bukaci ‘yan jam’iyya su kaurace wa taron, yana mai cewa PDP za ta yi cikakken taro ne a lokacin da doka ta gamsar da su — ba a cikin rikicin da ya Ĉ™ara zurfafa rarrabuwa ba.

A gefe guda, Ministan FCT Nyesom Wike ya jinjinawa magoya bayansa, yana mai cewa sun tsaya tsayin-daka wajen “kare jam’iyya” duk da matsin lamba da suka fuskanta. Ya sha alwashin ci gaba da goyon bayansu tare da kare abin da ya kira gaskiya da doka.

A yayin da ake tattaki tsakanin kotuna, bangarori, da kuma fafatawar iko, wannan mataki na korar manyan jiga-jigan jam’iyyar ya sake jefa PDP cikin sabon tarihi — ko dai ya ɗaure ta, ko kuma ya wawashe ginshikan haɗin kai gaba ɗaya.

No comments