Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ko Janar Ba Ya Marin Soja — Janar Irabor Ya Gargaɗi Wike

Tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya caccaki Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan rigimar da ta...



Tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya caccaki Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan rigimar da ta shiga tsakaninsa da Laftanar A.M. Yerima, jami’in sojan ruwa da ya tsoma baki yayin rusau da aka gudanar a Abuja saboda batun fili.

A wata hirar da aka yi da shi a shirin AIT Live News daga 4:11, Janar Irabor ya yi Allah-wadai da kalaman Wike na cin mutunci, yana mai cewa jami’an da ke sanye da kaki na wakiltar ikon Jamhuriyar Nijeriya, don haka dole ne a girmama su.

Ya jaddada cewa, ladabi da bin doka su ne ginshiƙan rundunar soji, inda ya bayyana cewa ko shi da yake Janar, ba shi da ikon mari ko taɓa mutumcin soja koda ƙaranin jami'i ne.

Ya ce, “Ni a matsayina na Janar, ba zan iya marin sojana ba, ba zan iya taɓa shi ba. Idan na yi hakan, sai dai na nemi afuwarsa ko kuma a hukunta ni.”

Irabor ya nuna cewa tsarin da rundunar soji ta gindaya yana tabbatar da ɗa’a, ladabi da mutunta juna, don haka bai kamata manyan jami’ai ko fararen hula su ci mutunci masu kaki ba.

Ya bayyana cewa duk wani kalaman batanci ko cin zarafi ga jami’in tsaro ba wai cin fuskar mutum ɗaya bane kaɗai ba — cin fuskar ikon shugaban ƙasa ne, wanda shi jami’in ke wakilta.

No comments