Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ba Za A Taba Samun Tsaro A Zamfara Ba Sai Da Ni — Matawalle

Taƙaddama tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Zamfara kan dabarun tsaro ta sake sabon salo, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, y...



Taƙaddama tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Zamfara kan dabarun tsaro ta sake sabon salo, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya zargi gwamnan jihar, Dauda Lawal, da ƙoƙarin yin watsi da shi.

Ya gargaɗi cewa duk wani yunqurin tsaro da ba a saka shi a ciki ba “ba zai haifar da komai ba.”

Ya yi waɗannan zarge-zargen ne a wata hira da DCL Hausa.

Matawalle, wanda ya yi wa’adin shekaru hudu a matsayin gwamnan Zamfara kafin a naɗa shi minista, ya ce Gwamna Lawal da gangar ya ƙi neman sa a lokacin da ya ziyarci ministan tsaro a Abuja duk da cewa kuwa yana ofis a lokacin.

“Ina wakilin Zamfara a gwamnatin tarayya,” inji shi ga DCL Hausa. “Ya kauce min ya je wurin Badaru. Zan iya faɗa muku hakan ba zai haifar da komai ba.”

Gwamna Lawal ya sha bayyana yadda halin tsaro ya tabarbare a Zamfara, yana mai cewa ya san mafakar ƙungiyoyin ‘yan bindiga, kuma zai iya kawo warshen matsalar cikin wata biyu — muddin jihar na da ikon umartar jami’an tsaro.

Gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ke aiki a jihar da cewa sau da yawa ba sa ɗaukar mataki sai da umarni daga Abuja — lamarin da ya ce na kawo cikas wajen kare rayukan jama’a.

Gwamna Dauda Lawal na kokarin ganin an samar da ingantaccen tsaro a jihar, wanda hakan ya sa ya sama da Rundunar Kare Al’umma, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Askarawan Zamfara’.

Zargin da Bello Matawalle ya yi na ɗauke da nauyin siyasa sosai, inda ya zargi wasu ’yan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da haɗa kai da vangaren Gwamna Dauda Lawal domin haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar. Matawalle ya yi gargaxin cewa mutanen da ke ɗaukar nauyin tayar da tarzoma a cikin APC ba za su daɗe cikin inuwa ba, domin a cewarsa, ba da jimawa ba za a fallasa su.

No comments