Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zamanin Rusa Gidaje Da Korar Ma’aikata Ya Ƙare A Jihar Kaduna.- Maiyaki

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an kawo ƙarshen zamanin rusa gidaje ba bisa ƙa’ida ba, korar ma’aikata barkatai, da sauran abubuw...


Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an kawo ƙarshen zamanin rusa gidaje ba bisa ƙa’ida ba, korar ma’aikata barkatai, da sauran abubuwan da ke haifar da tsoro da rashin tabbas cikin jama’a.

Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin  Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, yayin ziyarar ƙarfafa haɗin gwiwa da ya kai  gidajen  rediyon Vision da Maria a Kaduna.

Ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani ta ƙuduri aniyar tafiyar da mulki cikin tausayi tare da maida al’umma a gaba.

Maiyaki ya jaddada cewa gwamnatin jihar na son kauce wa manufofin da a da suka raba iyalai da muhallansu kuma suka lalata rayuwar mutane.

“Zamanin rusa gidaje, korar ma’aikata bisa son rai, da tsoratar da jama’ar mu ya wuce. Gwamna Uba Sani yana gina sabuwar hanya mai cike da zaman lafiya, ci gaba da mutunta ‘yan ƙasa,” in ji shumma

A cewar sa, jajircewar gwamnati wajen ƙara buɗe zumunci da kusantar jama’a ne ya sa aka dawo da Ma’aikatar Yaɗa Labarai, wadda gwamnatin da ta gabata ta soumma.

Ya yi kira ga kafofin watsa labarai su riƙa neman cikakken bayani daga gwamnati a kan lamurra don kauce wa yaɗa bayanan ƙarya da kuma goyon bayan ƙoƙarin sake gina amana tsakaninsu da al’umma.

Maiyaki ya kuma  bayyana nasarorin Kaduna akan Sabon tsarin samar da zaman lafiya da tsaro wanda ake danganta masa raguwar ayyukan ‘yan bindiga da dawo da kwanciyar hankali a kananan hukumomi kamar Birnin Gwari, Chikun, Kajuru, Kauru, Kachia da Giwa.

Shugaban Ma’aikatan gidan rediyon Vision Malam Abdulhamid Idris, ya yaba da wannan sabuwar alaka, tare da tabbatar da cewa gidan rediyon na shirye wajen tallafa wa duk wani yunkuri da ya shafi ci gaban al’umma.
 

No comments