Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SAMAR DA ISASSHEN ABINCI: Nasarawa Na Neman Samar Da Buhun Shinkafa Miliyan 1.2 Daga Gonakin Gwamnati

  Daga Zubairu  Lawal Lafia  Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa a ranar Alhamis ya bayyana cewa jihar na kokarin samar da fiye da buhun...


Daga Zubairu  Lawal Lafia 

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa a ranar Alhamis ya bayyana cewa jihar na kokarin samar da fiye da buhun shinkafa miliyan 1.2 daga gonakin shinkafa mallakin gwamnati da ke Jangwa da Agwatashi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a Karamar Hukumar Awe yayin zagayen duba aikin girbin shinkafa da ake gudanarwa.

Sule, wanda ya nuna farin ciki kan girbin da aka fara kusan makonni biyu da suka gabata, ya bayyana cewa tuni an girbe fiye da buhunan shinkafa 600,000, yana mai ƙara da cewa za a samu ƙarin buhuna cikin makonni biyu masu zuwa lokacin da za a kammala girbin gaba ɗaya.

An tuna cewa gwamnatin jihar ta saya kadada 10,000 domin noman shinkafa, amma kadada 3,300 ne kacal aka noma a bana.

Ya ce gwamnatin na shirin noma ƙarin fili—ko ma duka filayen—a kakar noman da ke tafe.

Gwamnan ya ƙara da cewa jihar ta fara jigilar shinkafa daga gona zuwa Abuja da Lokoja a Jihar Kogi domin nika da yin kwalliya.

Sule ya bayyana cewa jihar ta shiga haɗin gwiwa da kamfanin sarrafa shinkafa na Silvex International, wanda ya yi fice a fannin sarrafa shinkafa a ƙasar.

Ya ce wannan haɗin gwiwa ya shafi yadda Silvex International za ta rika sayen shinkafa kai tsaye daga gonar gwamnati sannan ta rika sanya ta a ƙarƙashin alamar kamfanin Nasarawa Agro-Commodity Company (NASACCO).

A cewarsa, shinkafar—wadda za a sayar da ita da sunan “NASACCO Gold”—za ta ƙara fito da kayayyakin shinkafar jihar a kasuwa tare da inganta batun samar da isasshen abinci a ƙasar.

“Zamu kaddamar da shinkafar NASACCO a Abuja nan ba da jimawa ba bayan an kammala girbin bana da nika,” in ji Sule.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala girbi, gwamnati za ta fara share sauran filayen don shirye-shiryen kakar noma ta gaba.

Sule ya bayyana cewa jihar ta tanadi dukkan kayan aiki da tsare-tsare da za su tabbatar da dorewar aikin gonakin bayan wa’adin wannan gwamnatin, ganin muhimmancinsa ga samar da abinci da ayyukan yi saboda tsawon sarkar darajar da ya ƙunsa.

Ya gode wa al’ummomin yankin, jami’an tsaro, ma’aikatan gwamnati, abokan hulɗa, da ma’aikatan gona bisa gudunmawar da suka bayar tun farkon kakar noma har zuwa lokacin girbi.

Gwamnan ya kuma ce jihar ta daidaita da shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na sauya tsarin aikin gona domin samar da ayyukan yi da wadatar abinci a fadina
 

No comments