Rahotanni daga Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane aƙalla bakwai a wani rikici tsakanin wasu masu ha...
Rahotanni daga Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane aƙalla bakwai a wani rikici tsakanin wasu masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ’yan bindiga.
Wani mazaunin yankin, Umar Maishanu, ya shaida wa gidan talbijin Channels cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Alhamis a yankin Kuyello, wanda ke gabashin Birnin Gwari, kusa da iyakar jihohin Zamfara da Katsina.
A cewar Maishanu, rikicin ya fara ne bayan wani ɗan bindiga daga Zamfara ya iso wajen hakar ma’adinan domin karɓar kuɗin haraji daga wajen su, sai suka kashe shi suka binne gawar sa.
Wannan ya fusata abokan sa ’yan bindiga, inda suka dawo da yawan gaske don ramuwar gayya, suka kai hari kan wurin hakar ma’adinan, suka kashe mutane bakwai cikin su.
Kodayake rundunar ’yan sanda ba ta tabbatar da lamarin ba tukuna, majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa an tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa zuwa wajen domin daƙile ƙarin tashin hankali.
Rahoton ya kuma nuna cewa an kama wasu daga cikin ’yan bindigar da suka fito daga Zamfara bayan artabu.
Lamarin ya faru ne kusan shekara guda da aka samu zaman lafiya a yankunan Birnin Gwari, Giwa, da Igabi, sakamakon tsarin sulhu da gwamnatin jihar ta ƙaddamar don dawo da harkoki na yau da kullum kamar makarantu, kasuwanni da asibitoci.
Sai dai bayan wannan sabon hari, mazauna yankin sun roƙi gwamnatin jihar da ta hana duk wani nau’in haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Birnin Gwari, domin hana sake tayar da tarzoma da tada hankalin jama’a.
A gefe guda, Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata ya bayyana cewa haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban yanki. Ya yi kira ga shugabannin kasashen Yammacin Afirka da su ɗauki wannan aiki a matsayin babban laifi na ƙasa-da-ƙasa.
Tinubu ya ce, “Lokaci ya yi da za mu ɗauki sata da fasa ƙwabrin albarkatun ƙasa a yankinmu a matsayin laifi na duniya, domin yana barazana ga zaman lafiya da ci gaban Afirka ta Yamma.”

No comments