Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Rubuta Wasiyyar Ku Tun Da Wuri – Gwamna Otti Ga Masu Shirin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya gargaɗi duk wanda ke shirin yin maguɗin zaɓen gwamnan jihar a shekarar 2027 da su “rubuta wasiyyar su tun ...



Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya gargaɗi duk wanda ke shirin yin maguɗin zaɓen gwamnan jihar a shekarar 2027 da su “rubuta wasiyyar su tun da wuri,” yana mai cewa jama’ar jihar ba za su yarda a tauye musu haƙƙin su ba.

Gwamna Otti ya bayyana hakan ne a lokacin taron sa na wata-wata da manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Umuahia, babban birnin jihar Abia, ranar Alhamis.

Ya ce gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani yunƙurin karkatar da sakamakon zaɓe ba, domin mutanen jihar sun waye kuma sun kuduri aniyar kare dimokuraɗiyya.

“Ina so in faɗi a fili — duk wanda yake tunanin zai iya rubuta sakamakon zaɓe a ofishin sa, ya fara rubuta wasiyyar sa. Mutanen Abia ba za su yarda da hakan ba,” in ji shi.

Otti, wanda ya lashe zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP), yana gudanar da zangon sa na farko na mulki mai tsawon shekaru huɗu.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan harkokin siyasa da gudanarwa, tare da tabbatar da cewa ‘yan Abia ne ke yanke makomar jiharsu ta hanyar kuri’a, ba ta hanyar maguɗi ko barazana ba.

No comments