Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kama Mahaifi Da Zargin Yi Wa ’Yarsa Fyaɗe A Ondo

Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Ondo ta kama wani mutum mai matsakaicin shekaru da ake zargi da yin fyaɗe ga ’yar sa mai shekaru 15 a ƙauyen Aj...



Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Ondo ta kama wani mutum mai matsakaicin shekaru da ake zargi da yin fyaɗe ga ’yar sa mai shekaru 15 a ƙauyen Ajue, ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Oyewole Adamolekun, ya daɗe yana lalata da ’yarsa tun tana da shekara uku, har ta balaga.

Rahoton ya nuna cewa wani mazaunin yankin ne ya kai ƙorafi ga ofishin ‘yan sanda na Enu-Owa a garin Ondo, inda jami’an suka kama wanda ake zargin nan take.

“An kai yarinyar asibiti don gwaji, kuma sakamakon binciken likitoci ya tabbatar da cewa tana ɗauke da juna biyu makonni 19 da kwanaki biyu,” inji DSP Ayanlade.

Ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifin nasa yayin bincike, inda aka miƙa shari’ar zuwa sashen kula da harkokin mata na rundunar domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a kotu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adebowale Lawal, ya la’anci lamarin da cewa babban laifi ne kuma abin ƙyama ga ɗabi’a da al’adu, yana mai tabbatar da cewa za a tabbatar da adalci cikin gaggawa da bin ƙa’ida.

“Wannan laifi ne mai muni da bai kamata ya sami wuri a cikin al’umma ba. Za mu tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargi yadda doka ta tanada,” inji Kwamishinan.

No comments