Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta gano manyan ma’adinai da suka haɗa da zinari, tagulla da litium a wasu yankuna na jihar, sakamakon...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta gano manyan ma’adinai da suka haɗa da zinari, tagulla da litium a wasu yankuna na jihar, sakamakon ƙoƙarin Gwamna Uba Sani wajen bunƙasa sashen ma’adinai da tattalin arzikin cikin gida.
Manajan Darakta na Kamfanin Harkokin Ma’adinai na Jihar Kaduna (KMDC), Injiniya Shuaibu Kabir Bello, ne ya bayyana hakan yayin Taron Makon Ma’adinai na Nijeriya (Nigeria Mining Week 2025) da aka gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga Oktoba a birnin Abuja.
A cewarsa, an gano waɗannan ma’adinai ne a yankin Gidan Waya da ke ƙaramar hukumar Jema’a, inda binciken ya tabbatar da kasancewar adadin tan 97 na ma’adinai masu daraja.
Injiniya Bello ya ce an gudanar da binciken ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Kamfanin Kian Smith, Hukumar Kula da Ma’adinai ta Jihar Kaduna, da Kamfanin Anka Metals JV, bayan shekaru biyu na bincike mai zurfi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙirƙiri sabon tsarin kula da albarkatun ƙasa wanda zai tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a fannin ma’adinai. Haka kuma, an kafa Kwamitin Fasaha domin lura da ayyukan haƙa da tabbatar da sahihancin adadin ma’adinai da ake dasu a jihar.
> “Gano wadannan ma’adinai, musamman ma Nickel, muhimmin ci ne ga ƙasa da kuma fannin ilimin ƙasa,” in ji Injiniya Bello.
Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, kasancewar ita ce ke da ikon tattara da tabbatar da bayanan ma’adinai a fadin ƙasa.
A cewarsa, NGSA ta yaba da yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke gudanar da ayyukan ta cikin gaskiya da bayyana bayanai a fili, tare da shawartar a gudanar da bincike mai zaman kansa domin ƙara tabbatar da ingancin sakamakon.
Injiniya Bello ya ce wannan haɗin gwiwa zai buɗe ƙofofin sabbin saka jari a sashen ma’adinai, tare da ƙarfafa tattalin arzikin jihar da ƙasar baki ɗaya ta hanyar faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa da bunƙasa masana’antun cikin gida.
Kwamitin Fasaha da aka kafa ya haɗa da manyan kamfanonin bincike na cikin gida irin su GES da FISAS.


No comments