Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Haɗakar 'Yan Adawa Cike Ta Ke Da 'Yan Siyasar Da Ba Sa Kishin Al’umma, Babu Tasirin Da Za Ta Yi -Abdulaziz Abdulaziz

Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana yunƙurin kafa jam’iyyar haɗakar a...


Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana yunƙurin kafa jam’iyyar haɗakar adawa da wasu ’yan siyasa ke jagoranta a matsayin yunƙuri mara tasiri, yana mai cewa shugabannin haɗakar ba mutane ne da tasirin siyasar su ya jima ta ƙarewa kuma ba su da ƙimar siyasa a idon jama’a.

Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ’yan jarida a cibiyar Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) reshen Kano a ranar Talata, in da ya bayyana waɗanda ke jagorantar ƙungiyoyin a matsayin “’yan siyasa da ba sa kishin al’umma, waɗanda ke motsi kawai don huce haushin rashin samun muƙami.”

“Ina tabbatar muku cewa shugaban ƙasa bai da wani ɗar. Ba ya cikin damuwa game da kowace irin jam’iyya ko haɗaka. Domin jagororin haɗakar sun daɗe da rasa tasiri a siyasa. Sun sha tsayawa takara suna faɗuwa. A yanzu ma tauraruwar su na ƙarasa dusashewa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Waɗannan mutane ba damuwar talakawa ce a gabansu ba. Damuwarsu ita ce rashin samun kujerar mulki. Kuma ’yan Nijeriya sun riga sun fahimci hakan, shi ya sa wannan haɗaka ba ta yi tasiri kamar yadda suka zata ba.”

Abdulaziz ya bayyana cewa shugabancin Tinubu ya fi karkata kan ɗaukar matakan gyara masu wahala amma masu amfani, ba wai bin tsarin neman farin jini ba tare da samar da mafita ba.

“Akwai bambanci tsakanin shugabanci da siyasa. Siyasa fagen neman farin jini ce, shugabanci kuwa aikin gina ƙasa ne. Kuma wannan shi ne abin da Shugaba Tinubu ke yi. Yana ɗaukar matakai masu tsauri, ko da zai shafi kansa, muddin ya ga cewa zai amfani ƙasar,” in ji shi, 

Dangane da koke-koken da ake yi cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali kan ayyuka a kudu, Abdulaziz ya ce maganganu ne kawai na siyasa, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasa na ci gaba da manyan ayyuka a Arewa da ya gada, ciki har da aikin bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano, babban titin Abuja–Kaduna–Kano da kuma layin dogo na Kano–Katsina–Maradi.

“Ina so ku sani, idan da wannan mutum (Shugaba Tinubu) zai nuna wariya ko kyama ga Arewa, da ya bar waɗannan ayyuka su mutu. Amma ya ci gaba da bada kuɗi don a aiwatar da su, kuma ana cigaba da aiwatar da su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta kuma fara sabbin ayyuka kamar titin Sokoto–Badagry wanda yake daga manyan ayyukan da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ke yi dan bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya.
 

No comments