Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da 'Yan Bindiga Ta Taimaka Mana A Birnin Gwari -Sarki Maigwari

 Ganin yadda al'amuran harkokin yau da kullum suka fara dawowa kamar yadda suke a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, Sarkin Birnin Gwa...


 Ganin yadda al'amuran harkokin yau da kullum suka fara dawowa kamar yadda suke a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya yaba da nasarar tsarin zaman lafiya da aka ƙaddamar a yankin kusan watanni goma da suka gabata, inda ya bayyana cewa shirin ya dawo da kwanciyar hankali tare da ƙarfafa wa manoma gwiwa wajen komawa gonakin su.

Sarkin ya samu wani lokaci, inda ya zagaya Birnin Gwari, ya ce yarjejeniyar zaman lafiyar da ta samu da haɗin gwiwar mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Gwamnatin Jihar Kaduna, hukumomin tsaro da kuma wakilan ƙungiyoyin ’yan bindiga, ya taimaka sosai wajen rage matsalar rashin tsaro a yankin.

Ya ce duk da yake har yanzu ana samun 'yan ƙwace ƙwace daga wasu miyagu, amma dai lamarin tsaron ya yi sauƙi sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Sarkin ƙara haske da cewa a tarukan da aka gudanar da shugabannin al’umma, an shawarci manoma su koma gonakin su duk da ƙalubale, ko da hakan na nufin amfani da taki na gargajiya a maimakon na zamani.

A cewar sa, da dama daga cikin manoma sun bi wannan shawara, abin da ya haifar da dawowar ayyukan noma a yankin saboda zaman lafiya da aka samu.

Alhaji Zubairu Maigwari ya jaddada cewa nan da shekara mai zuwa, ana sa ran ƙarin manoma za su koma cikakke gonakin su idan zaman lafiya ya ci gaba da inganta.

Ɗanmasanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu AbdurRauf, ya bayyana cewa tsarin zaman lafiyar ya samar da damar zama tare, inda makiyaya da manoma ke aiki tare domin kare wannan yarjejeniya.

Ya ƙara da cewa harkokin tattalin arziki sun fara farfaɗowa a Birnin Gwari, inda al’ummomi da kansu ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ya kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna su faɗaɗa tsarin zuwa wasu wurare masu fama da rikice-rikicen, musamman ƙauyukan kan iyaka da ke fuskantar barazanar shiga daga jihohin maƙwabta.

Ya jaddada cewa irin tsarin tabbatar da zaman lafiya da aka yi a Birnin Gwari zai taimaka wajen daƙile matsalolin tsaro a yankunan kan iyaka tare da ƙarfafa ƙoƙarin zaman lafiya a fadin ƙasar nan.

Bayanai na nuni da cewa yammacin Birnin Gwari, ciki har da Dam ɗin Fagoma da Sabon Layi da Gagumi da Kakangi da Kuma Randagi sun suka koma gonakin su.

A matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar, tsoffin ’yan bindiga da al’ummomin yankin ana sa ran za su tashi tsaye domin kare yankin su daga dukkan wani kaluiubalen tsaro.

No comments