Daga Ashafa Murnai Barkiya Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara aiki da kasafin 2025 a cikin watan Satumba. Babban Darakta na Ofishin...
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara aiki da kasafin 2025 a cikin watan Satumba. Babban Darakta na Ofishin Kasafin Kuɗaɗe na Tarayya, Tanimu Yakubu ne ya tabbatar da haka, yana mai cewa a ƙarshen Satumba za a fara aiki da kasafin, yayin da aka kawo ƙarshen aiki na tsare-tsaren kasafin 2024.
Yakubu ya yi wannan ƙarin haske ne lokacin da yake jawabi a taron ganawa da masu ruwa da tsaki kan kasafi da kuma jama'a da ƙungiyoyi, wanda Ma'aikatar Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare Tattalin Arziki ta Kasa ta shirya, ranar Alhamis a Abuja.
Babban Daraktan ya ci gaba da cewa an tsara kasafin 2025 na Naira tiriliyan 54.99, wanda aka yi wa take da Kasafin FarfaÉ—o da Tattalin Arziki, domin a zaburar da harkokin tattalin arziki, ayyuka sannan kuma da jawo É—imbin masu zuba jari a fannoni daban-daban.
"Za a fara aiki da kasafin kuɗaɗe na 2025 a ƙarshen Satumba. An tsara kasafin domin ya magance muhimman ɓangarori, inganta tattalin arziki da kuma ƙarfafa ayyukan gwamnati. Za a riƙa aiwatar da ayyukan kashe kuɗaɗe bisa taka-tsantsan, domin tabbatar da samun nasarar da ake buƙatar samu," inji Yakubu.
Daga nan ya yi magana kan muhimmancin 'yan Najeriya su riƙa shiga a harkokin ayyukan kasafin kuɗaɗe, yana mai cewa a ƙarshe dai 'yan Najeriya ɗin ne za su moriyar duk wasu albarkatun ayyukan da gwamnati ta samar.
Ya ce ana nan ana ƙoƙarin ganin an fassara dukkan bayanan kasafin kuɗaɗe zuwa yarukan cikin gida, ta yadda za a sauƙaƙa wa jama'a fahimtar kalmomi masu sarƙaƙiya. Ya ce yin hakan zai sa jama'a su fahimci gundarin abin da kasafin ya ƙunsa ɗungurugum, tare sa-ido sosai kan yadda gwamnati ke aiwatar da ayyukan da ke ƙarƙashin kasafin.
Da ya ci gaba da bayani, Yakubu ya bayyana irin ƙalubalen da suka dabaibaye tsare-tsaren gudanarwar kuɗaɗen gwamnati a Najeriya, waɗanda ya ce sun haɗa da: matsalar kasa daidaita takamaiman hasashen kuɗaɗen shigar da gwamnati za ta samu daga man fetur da dangogin sa, matsalar da ke tattare da aiwatar da Dokar Man Fetur ta 'Petroleum Industry Act', inganta sahihancin hanyoyin tara kuɗaɗen haraji da tsarin biyan kuɗaɗen gwangiloli, sai kuma ɗimbin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen biyan basussuka.
Ya yi nuni da cewa aƙalla Naira tiriliyan 14.3 duk wajen biyan basussuka za ta tafi daga cikin kasafin 2025.
A ƙarshe ya bayyana matakan da za a ɗauka domin mara wa gwamnati baya, ta yadda za ta bunƙasa tattalin arzikin Najeriya har ya kai gejin Dala tiriliyan ɗaya, nan da zuwa shekarar 2030.
Ya ce cikin matakan da za a ɗauka har da tsare-tsaren ciyar da mazaɓun faɗin ƙasar nan su 8,809 gaba, gyaran tsarin haraji, taka-tsantsan da sa-ido wajen kashe kuɗaɗe, sai kuma haɗin guiwar bunƙasa tattalin arziki, kamar irin shirin haɗin guiwa tsakanin Najeriya da Japan na Dalar Amurka miliyan 30.9.
A jawabin sa, Ministan Kasafin Kuɗaɗe Abubakar Bagudu, ya tabbatar tare da jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki da gaskiya tare da amfani da bayyanannun hujjojin ƙididdiga ba shaci-faɗi ba.
Ya ci gaba da cewa tuni an fara aiki da kuɗaɗen kasafin 2025 a ɓangaren ayyukan gudanarwar gwamnati, irin su biyan albashi da kuma biyan basussuka da ake kan yi.
No comments