Daga Ibrahim Muhammad, Kano Hon. Kabiru A.D Domestic, mataimaki ne na musamman ga Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad akan harkar ciki...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hon. Kabiru A.D Domestic, mataimaki ne na musamman ga Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad akan harkar cikin Gida, wato 'P.A Domestic,' ya samu gagarumar karramawa daga ƙungiyar ci gaban Ɗambatta da Makoɗa ta jihar Kano, bisa irin gudumawar da ya ke bayarwa a yankin.
Da ya ke tofa albarkacin bakin sa bisa wannan karimci da aka yi masa, Hon. Kabitu ya bayyana jin daɗin sa, wanda ya ce an yi masa ne bisa irin tallafin da suka ga yana yi ga ci gaban Ƙananan Hukumomin su.
Ya ce karramawar za ta ƙara masa karsashi da sake yin hobbasa wajen ci gaba da ayyuka na alheri da yake aiwatarwa, inda ya ce yanzu zai nunka fiye da abubuwan da yake yi a baya, domin in har al'umma sun ga ka yi abin alheri suka karrama ka a kai, to ka ƙara ƙoƙari.
Hon. Kabiru P.A Domestic ya ce, duk da cewa shi ɗan asalin Ɗanbatta ne da yake zaune a jihar Bauchi, suna zaman lafiya da har yake bayar da gudumawa na alkheri a siyasar jihar, kasancewar Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir sananne ne a Nijeriya baki ɗaya wajen ayyukan alheri.
Ya ƙara da cewa, suna tafiya tare da Gwamnan Bauchi Sanata Bala, duba da irin alhairan sa, domin shi mutum ne da yake yin ɗimbin ayyuka na ci gaban al'umma, kuma da yardar sa suke bayar da gudumawa ga jihar Bauchi, har suke bada gudumawa na alheri da ya shafi Ɗambatta da Makoɗa.
Hon.Kabiru ya ƙara cewa daga irin abubuwan alkheri da ƙungiyar ci gaban Ɗanbatta da Makoɗa suka ga yana yi har suka karrama shi, daga ciki akwai gina masallatai, taimaka wa marayu da sauran mutane masu ƙaramin ƙarfi, ta hanyar gyara musu muhallai da suka rushe, da taimaka wa makarantu na Islamiyya da na zamani, da taimakon buƙatun matasa a fannonin gina ci gaban rayuwar su.
No comments