Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar ...
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja a ranar Litinin. Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.
A cewar rahoton, bangaren noma ya samu ci gaban kashi 2.82 idan aka kwatanta da kashi 2.60 da aka samu a zango na biyu na 2024. Bangaren masana’antu ya samu ci gaban kashi 7.45, wanda ya ninka kashi 3.72 da aka samu a zango na biyu na 2024. Bangaren ayyuka kuma ya samu kashi 3.94 idan aka kwatanta da 3.83 na zango na biyu na 2024.
Rahoton ya ce a cikin zango na biyu na 2025, darajar GDP ta kai Naira tiriliyan 100.73, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 84.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, wanda ya nuna ci gaban shekara zuwa shekara da kashi 19.23.
Haka kuma, bangaren mai ya samu ƙarin kashi 6.01 a zango na biyu na 2025 idan aka kwatanta da zangon farko na 2025. Bangaren ya bayar da gudummawar kashi 4.05 cikin ɗari ga GDP, idan aka kwatanta da kashi 3.51 na zango na biyu na 2024 da kuma 3.97 na zangon farko na 2025.
Rahoton ya kuma nuna cewa matsakaicin adadin fitar da man fetur ya kai ganga miliyan 1.68 a kullum a zango na biyu na 2025, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.41 da aka samu a zango na biyu na 2024, da kuma ganga miliyan 1.62 a zangon farko na 2025.
No comments