Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York domin halartar zaman taro na 80 na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda z...

An tarbe shi a filin jirgin sama na John F. Kennedy inda ya samu rakiyar ministoci da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar.
Shettima, wanda yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi a madadin Nijeriya a taron, tare da halartar muhawarorin manyan shugabanni da kuma wasu tarurruka a gefen taron Majalisar.
Haka kuma, zai sanar da sabbin ƙudirin Nijeriya na rage dumamar yanayi (NDCs) ƙarƙashin yarjejeniyar Paris, tare da shiga tattaunawa kan samar da gidaje masu araha, tsaro da zaman lafiya, da kuma wasu muhimman yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashe.
Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya na ɗaukar nauyin jagorancin ƙoƙarin kafa dokar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haraji, tare da matsa lamba kan batun sake fasalin kwamitin tsaro na MDD domin ba wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin.
A cewar sa, wannan zai tabbatar da cewa muryar Afirka ta karade duniya, yayin da Nijeriya kuma ke amfani da damar wajen jawo hannun jari a bangarorin ma’adinai, noma, fasaha da sauran manyan sassa na tattalin arziki.
No comments