Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SAYAR DA MAKAMAI: An Yanke Wa Sojojin Nijeriya Huɗu Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai

Wata kotun soji a Nijeriya ta yanke wa sojoji huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri...



Wata kotun soji a Nijeriya ta yanke wa sojoji huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kotun ta fitar, shugaban Kotun, Brigadier Janar Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari.

Wannan hukunci ya biyo bayan amincewar su kan aikata laifuffukan da suka haɗa da "sata da kasuwancin makamai ba bisa ka’ida ba, da taimaka wa maƙiya" wanda duka laifuka ne ƙarƙashin dokar sojojin Nijeriya.

Kotun ta bayyana cewa "irin wannan safarar da ba bisa ƙa’ida ba na zamewa haɗari ga sojoji da ayyukan soja, da kuma tsaron ƙasa, don haka yana nufin taimaka wa maƙiyan ƙasar".

Shugaban Kotun, Brigadier Janar Abdullahi, ya ce waɗannan laifuka da sojojin suka aikata ba matsala ce kawai ta karya doka ba, har ma da cin amana, da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci irin waɗannan rashin ɗa’a da halayen damfara ko rashin kwarewa ba.

Borno ce cibiyar rikicin Boko Haram da Nijeriya ta kwashe kimanin shekara 15 tana fama da shi, lamarin da ya laƙume rayukan dubban mutane da haifar da matsalar jin-ƙai.

No comments