Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana wa masu zuba jari na ƙasashen waje cewa Nijeriya na da damar zuba jari mai darajar sam...


Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana wa masu zuba jari na ƙasashen waje cewa Nijeriya na da damar zuba jari mai darajar sama da Dala Biliyan 200 a fannin makamashi.

Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da Ƙungiyar Kasuwanci ta Ƙasa da Ƙasa (Business Council for International Understanding – BCIU) ta shirya a birnin New York, Amurka, gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.

Shettima ya ce Nijeriya na buƙatar haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin cin gajiyar wannan dama, musamman a fannonin makamashi na zamani. Ya ce Nijeriya na da mai da iskar gas mafi yawa a Afirka, da kuma hasken rana mai ƙarfi fiye da ƙasashe da dama a nahiyar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.

Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi.

Shettima ya ce: “Nijeriya ita ce babbar tattalin arzikin Afirka ta Yamma, kuma tana da kasuwa mafi girma a nahiyar, inda al’ummarta ke kaiwa miliyan 236 yanzu, ana sa ran za ta kai miliyan 320 nan da 2040.”

Ya kuma bayyana cewa Najeriya tana da matasa da yawa, sama da kashi 58 cikin ɗari ‘yan ƙasa da shekaru 30 ne, lamarin da ya ce ke baiwa ƙasar manyan hazikai a fannoni daban-daban, ciki har da fasahar zamani.

Shettima ya yi kira ga masu zuba jari da su yi amfani da wannan damar, yana mai cewa Najeriya na kan gaba wajen zama cibiyar kasuwanci da kirkire-kirkire a nahiyar Afirka, tare da kasancewa babbar hanyar shiga kasuwar AfCFTA mai darajar dala tiriliyan 3.4.

A gefe guda, Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Olajumoke Oduwole, ta ce tun bayan shekarar 2023 gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki, kuma hakan ya fara kawo canje-canje da inganta halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Ta ce “a halin yanzu, akwai fiye da dala biliyan 50 daga masu son zuba jari da aka tattara a fannoni daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.”

Shettima ya yi wannan bayani ne jim kaɗan bayan ya halarci taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi na minti uku wajen tunawa da cikar Majalisar shekara 80 da kafuwar Majalisar.





 

No comments