Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kawo ƙarshen doka ta-ɓaci na tsawon wata shida da ya sanya wa jihar Ruvers da ke kudu maso kudancin ƙasar. Ciki...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kawo ƙarshen doka ta-ɓaci na tsawon wata shida da ya sanya wa jihar Ruvers da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Cikin wata sanarwa daga fadar shugaba ƙasar, ta ambato Tinubu na cewa dokar ta gma aiki daga tsakar daren yau.
''Don haka daga gobe Alhamis 18 ga watan Satumba, Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagoracin kakakin majalisar jihar, Martins Amaewhule, za su koma aikinsu'', inji Tinubu.
A ranar 18 ga watan Maris ɗin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar bayan rikicin siyasar jihar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin tsagin gwamnan jihar da na ministan Abuja, Nyesom Wike - wanda shi ne tsohon gwamnan jihar.
No comments