Hukumomin Saudiyya sun saki wasu ’yan Nijeriya uku da aka tsare a Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi Mutanen da aka saka su...
Hukumomin Saudiyya sun saki wasu ’yan Nijeriya uku da aka tsare a Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi
Mutanen da aka saka su ne Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq.
In dai ba a manta ba, a kwanakin baya Jaridar MATATTATAR LABARAI ta kawo labarin yadda wasu gungun ma'aikata da ke aiki a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu da ke Kano (MAKIA) da aka zargi da manna sunayen mutanen uku a wasu akwatuna da ke ƙunshe da miyagun ƙwayoyin.
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ce ta sanar wa manema labarai batun sakin mutanen uku, kamar yadda ita ce kuma ta fitar da wancan labarin.
Hukumar ta ƙara da cewa mutanen uku sun ɗauki akwatunan miyagun kwayoyin, bisa rashin sani, suka shiga jirgin Ethiopian Airline ET940 da ya bar Kano zuwa Jidda a ranar 6 ga watan Agusta, 2025, domin yin umara, wanda bayan isar su Jidda ne aka kama su.
Binciken da aka yi ya kai ga kama wani mai shekara 55 Mohammed Ali Abubakar da aka fi sani da Bello Karama, wanda shi ne jagoran waɗanda ake zargi da musanya akwatunan da wasu mutum uku, ciki har da ma'aikacin jirgin.
Tuni aka gabatar da tuhume-tuhume a kan mutanen da ake zargi, Mohammed Ali Abubakar da Celestina Emmanuel Yayock da Abdulbasit Adamu Sagagi da kuma Jazuli Kabir.
No comments