Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

LAMBAR GIRMAMAWA: Shugaba Tinubu Ya Taya Shettima Murna

  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mataimakin sa, Kashim Shettima, da wasu fitattun ’yan Nijeriya murna bayan an karrama su da lambar...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mataimakin sa, Kashim Shettima, da wasu fitattun ’yan Nijeriya murna bayan an karrama su da lambar girmamawa ta “Fellow” na Ƙungiyar Masana Tattalin Arzikin Nijeriya [Nigerian Economic Society (NES)] saboda rawar da suka taka wajen tsara manufofin tattalin arziki da bincike a fannin ci gaba.

A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa, an bayyana cewa an karrama su ne a ranar Litinin, 8 ga Satumba, a matsayin shaida ta irin gudummawar da suka bayar wajen sauya fasalin tattalin arzikin ƙasar.

Shugaba Tinubu ya yaba wa Shettima bisa hangen nesansa da jajircewarsa wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Renewed Hope Agenda, musamman a fannonin samar da ayyukan yi da kuma haɓaka tattalin arzikin da ya haɗa kowa.

Ya kuma jinjina wa Dr. Iyabo Masha, ƙwararriyar masaniyar tattalin arziki wacce a halin yanzu take jagorantar Ƙungiyar ƙasashe 24 a kan harkokin kuɗi na ƙasashen duniya da ci gaban tattalin arziki [Intergovernmental Group of Twenty-Four on International Monetary Affairs and Development (G-24)].

Shugaba Tinubu ya ce wannan lambar yabo da aka ba su abin alfahari ne ga ƙasar baki ɗaya, tare da zama abin koyi ga matasan masana da masu bincike a fannin tattalin arziki.

Ya bukace su da su ci gaba da amfani da ƙwarewarsu wajen tallafa wa shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, ƙarfafa ci gaban da zai haɗa kowa, da kuma tabbatar da cewa Nijeriya ta tsaya daram a gasar cigaban tattalin arziki a duniya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki tare da masana da cibiyoyi domin cimma ci gaba mai ɗorewa da yaƙi da talauci a tsakanin ’yan ƙasa.
 

No comments