Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

HARIN BAMA: Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ƙarin Ƙarfin Soji Domin Murƙushe 'Yan Ta'adda

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a wani sakon jajanta wa gwamnati da al'ummar Jihar Borno kan harin da ...


Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a wani sakon jajanta wa gwamnati da al'ummar Jihar Borno kan harin da 'yan ta'adda suka kai wa yankin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama. Harin, wanda aka kai a daren Juma'a, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da sojojin Nijeriya.

Shettima Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar kafa 'yan sandan jihohi domin tunkarar ƙalubalen tsaro a matakin farko.

Tuni gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci yankin da abin ya shafa a ranar Asabar domin jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa. 

Mataimakin Shugaban Kasar ya tabbatar wa da al'ummar jihar cewa za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatin tarayya a yakin da jahar ke yi da rashin tsaro.




 

No comments