Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Korar 'Yan Arewa Daga Abuja Ba Adalci Ba Ne -Gwamnatin Kano

 Daga Muhammad Ibrahim, Kano Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa da rashin jn daɗin ta bisa ci gaba da samu na korar jma'a marasa ƙarfi ...


 Daga Muhammad Ibrahim, Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa da rashin jn daɗin ta bisa ci gaba da samu na korar jma'a marasa ƙarfi daga Babban Birnin Tarayya Abuja, waɗanda ake maiyar da su zuwa Kano da sauran jihohin Arewa.

Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata ta Musamman ta jihar, Hajiya Amina Sani-Abdullahi ce ta yi wannan ƙoarafin cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kano.

Ta ce, gwamnatin jihar ta lura da cewa cikin makonni huɗu da suka gabata, an koro mutane da dama, ciki har da ‘yan asalin Kano, Jigawa, Katsina da Kaduna, waɗanda aka ɗebo daga Abuja.

A cewar ta, matakin da Hukumar Babban Birnin Tarayya ta ɗauka ya saba wa haƙƙin ‘yan Nijeriya na doka da ke ba kowa damar zama da neman abin yi a kowane ɓangare na ƙasar nan, muddin ba su zama barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a ba.

“Babban Birnin Tarayya ba mallakin wata jiha ko yanki guda ɗaya ba ne, don haka idan aka samu wasu mutane suna aikata ba-dai-dai ba, hanya mafi dacewa ita ce a sama musu abin dogaro da kai."

Ta ƙara da cewa ya kamata a samar musu da tallafi, ko kuma a ba su damar gyaran hali da samun aikin yi mai ma’ana, ba korar su  ba. 

A cewar ta, Kano na karɓar baƙi daga sassa daban-daban na Nijeriya, ciki har da Jihar Rivers da sauran yankuna, kuma suna zaune, suna aiki, tare da bada gudumawa ga tattalin arziƙin jihar, ba tare da nuna wani bambanci ba.

Kwamishiniyar ta kuma nuna damuwa kan bayanan da wasu daga cikin waɗanda aka kora suka bayar cewa sun shafe sama da kwanaki 10 a tsare cikin mawuyacin hali, inda ake ba su abinci sau ɗaya a rana, lamarin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da abin takaici ga tsarin Dimokraɗiyya.

Ta ce gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir-Yusuf ba za ta lamunci irin wannan tozarci ga ‘yan jihar ta ba, inda ta yi kira ga Hukumar ta birnin tarayya da ta kawo ƙarshen irin wannan korar karan da ake wa 'yan Arewa.

“Muna kira Hukumar FCT da ta sake duba tsarin ta, tare da ɗaukar matakai na doka, masu tausayawa da kuma amfani wajen shawo kan irin waɗannan matsaloli a gaba.” In ji ta.

No comments