Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar ƙananan ƙukumomin Ƙiru...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar ƙananan ƙukumomin Ƙiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa bisa zargin yin zagon ƙasa ga jam’iyya, da ƙin biyan kuɗin da doka ta tanada ga jam'iyya.
Shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi manema labarai.
Ya ce, an kafa kwamitin sulhu domin tattaunawa da Hon. Kofa bayan ya bayyana ra’ayin sa a kafar Talabijin na Channels, amma maimakon ya yi amfani da wannan dama, sai ya ci gaba da sukar jam’iyya da shugabannin ta.
Ya ƙara da cewa, har ma sai ya ci gaba da nuna adawa da jam'iyyar da nuna biyayya ga wasu na wajen jam’iyyar. Don haka suka yanke hukuncin korar sa, domin ba shi da wani ƙarin ƙima da zai kawo wa jam’iyyar.
Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce, ban da wannan, Kofa ya gaza biyan kuɗin da dokar da jam’iyya ta tanada, hakan zai iya jawo gurfanar da shi a kotu domin biyan kuɗin.
Daga nan ya yi nuni da cewa nasarar Hon. Kofa a zabe ba ta samo asali daga ƙarfin siyasar sa ba, illa kawai goyon bayan jam’iyyar NNPP da tasirin tafiyar Kwankwasiyya a ƙarƙashin jagorancin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Game da jita-jitar yiwuwar Hon. Abdulmumin Kofa ya koma jam’iyyar APC kuwa, Hon. Dungurawa cewa ya yi komawar sa ba zai taba kawo illa ga NNPP ba, domin siyasa haɗin kai ce kuma tafiyar Kwankwasiyya na nan daram tana tare da Kwankwaso.
No comments