Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Fitar Da Fursunoni 59 Albarkacin Kashim Shettima A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya  Ƙungiyar APC Youth Parliament, reshen Arewa maso Gabas ta 'yanto wasu fursunoni 59 daga gidan gyara hali na jiha...


Daga Khalid Idris Doya 

Ƙungiyar APC Youth Parliament, reshen Arewa maso Gabas ta 'yanto wasu fursunoni 59 daga gidan gyara hali na jihar Bauchi a ci gaba da bukukuwan taya mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima murnar cikar sa shekara 59 a duniya.

Kazalika, ƙungiyar ta rabar da tallafin kuɗaɗe ga marayu 59 dukka domin murna da ranar haihuwar mataimakin shugaban ƙasan, tare kuma da kai tallafin magunguna zuwa gidan gyaran hali da ke Bauchi.

Da ya ke jawabi a wajen bikin miƙa kyautatukan, a ranar Juma'a, shugaban ƙungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna godiya wa Allah bisa shekarun Kashim Shettima masu albarka waɗanda ya yi amfani da su wajen ci gaba da taimaka wa jama'a.

"Mun ɗauki adadin shekarun mataimakin shugaban ƙasa wato 59 wajen 'yanto Fursunoni da kuma raba kyautuka wa marayu daidai adadin shekarun mataimakin shugaban ƙasa a daidai lokacin da ake gaɓar komawa makarantu. Bayan wannan, mun kuma kai magunguna zuwa gidan gyaran hali dukka albarkacin mataimakin shugaban.

"Mun yi haka ne domin taimaka wa  marayun da ba su da galihu albarkacin Shettima kuma muka biya tara ga fursunonin 59 da suke gidan yarin domin su shaki iskar 'yanci dukka albarkacin Kashim."

Da ya ke magana kan Shettima, ya misalta shi a matsayin jagora na kwarai wanda ya himmatu wajen tabbatar da ci gaban yankin arewa maso gabas da ma ƙasar nan baki ɗaya. 

Kobi ya ce Shettima ya zama madubi wa matasa ta fuskancin zage damtse wajen hidima wa jama'a da ma ƙasar nan. 

Da ya ke jawabi kan muhimmancin taimaka wa marayu, wani malamin addini a jihar Bauchi, Imam Umar Yahuza Bauchi, ya ce, duk wanda ya taimaka wa maraya Allah zai taimaka masa, ya kuma nuna cewa taimakon Maraya ta ɓangaren ilimi na da gayar muhimmanci.

Ya yaba wa ƙungiyar kan hakan tare da kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen taimaka wa marayu a kowani lokaci.

Ita kuma Dr. Zuwaira Musa, masani a harkar ilimi a jihar, ta nuna muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfe ne wajen mayar da yara zuwa makaranta, ta ce, Bauchi na gaba gaba wajen fama da matsayar yara da ke fita daga makaranta wanda ta nuna hakan a matsayin babban illa ga ci gaba. 

Ta nemi iyaye da masu hannu da shuni da ke kai yara zuwa makaranta ta taimaka musu.

Wani jigon siyasa a jihar Bauchi, Kwamared Sabo Muhammad, ya shawarci ƙungiyar da ta ke irin wannan tarukan a sauran shiyyoyi da suke jihar Bauchi domin su ma su mori albarkacin Shettima.

Ya kuma yi gargaɗin cewa a yankin Arewa maso Gabas ba za su amince da dukkanin wani yunƙurin sauya mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe ba, ya nemi masu ruwa da tsaki a APC Da su tabbatar sun bar Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa don adalci da daidaita.

A gefe guda kuma ya shawarci al'umman jihar da maida hankali wajen sabunta katin zaɓensu domin a cewarsa ta haka ne kawai za su samu damar zaɓan wanda suke so a yayin zabe mai zuwa.

Ɗaya daga cikin fursunonin da aka sako, Bashir Ahmad, wanda a baya aka ci tarar Naira 30,000, ya bayyana godiya a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin ga matasan jam’iyyar APC da mataimakin shugaban ƙasa bisa samun ‘yancinsu da kuma ba su damar sake shaƙar iskar 'yanci.





 

No comments