Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Dawo Gida Bayan Kammala Babban Taron MDD

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya dawo Nijeriya bayan kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a bir...


Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya dawo Nijeriya bayan kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York, tare da wasu muhimman tattaunawa a ƙasar Jamus.

A yayin zaman mako guda na hulɗar ƙasashen duniya, Shettima ya gabatar da jawabin ƙasa na Shugaba Bola Tinubu inda ya yi kira ga cikakkun sauye-sauye a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Haka kuma, ya jagoranci kare ikon Afirka kan albarkatun ma’adananta da aka ƙiyasta darajarsu a dala biliyan 700 tare da ƙarfafa hulɗa ta dabarun cigaba da Birtaniya da Gidauniyar Gates, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a duniya.

Daga bisani, Shettima ya gana da shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, wanda ya yaba da yunƙurin Najeriya na neman kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar.

A wani zama ta daban kuma, Shettima ya gabatar da damar zuba jari a fannin sauyin makamashin Najeriya da darajarsa ta kai dala biliyan 200 ga manyan masu zuba jari na duniya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa al’ummar Najeriya mazauna ƙasashen waje cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da gana da su a harkokin gudanarwarta kafin ya wuce Jamus don kammala wasu muhimman hulɗoɗi.



 

No comments