Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bada tallafi na Naira biliyan 1.85 domin tallafa wa ilimi da gyaran rayuwa ga Yan Matan Chibok da aka...

Bisa bayanin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, daga cikin ‘yan Chibok da aka kubutar, 108 na Æ™arÆ™ashin kulawar gwamnati, inda 68 ke karatu a Jami’ar Amurka ta Nijeriya (AUN), dake Yola. Gwamnatin tarayya na ci gaba da biyan kuÉ—in makaranta, masauki da sauran haƙƙoÆ™in su.
An bayyana cewa shirin tallafin ya haÉ—a da, Kudin makaranta da masauki, Horar da Su sana’o’i da kayan fara aiwatarwa, Tallafin lafiyar kwakwalwa da ta jiki, Tallafin iyaye da yara, Kula da ci gaban karatu. Jimillar dukkan waÉ—annan tsare-tsare ya kai N1,854,277,768.
Ma’aikatar ta ce shirin ba wai tallafi na kuÉ—i kawai ba ne, yana nuna Æ™udurin Nijeriya na mayar da wannan munanan lamari cikin labarin jarumta, mutunci da kyakyawan fata.
Haka zalika, ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya nuna shugabanci nagari ta hanyar tabbatar da ci gaba da karatun ‘yan Matan Chibok a AUN duk da ya sami suka daga wasu ‘yan siyasa.
Tuni shekaru fiye da goma suka wuce tun lokacin da Boko Haram suka sace dalibai 276 daga Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Chibok, Borno, yayin da suke shirin kammala jarabawar karshe.
Ya zuwa yanzu, fiye da 178 sun samu kubuta ko sun tsere, amma fiye da 90 har yanzu ba a san inda suke ba.
No comments