Gwamnatin Tarayya ta ce kimanin gidaje 226,760 da ke cikin mawuyacin hali a jihar Nasarawa sun amfana daga shirin Household Prosperity and ...
Gwamnatin Tarayya ta ce kimanin gidaje 226,760 da ke cikin mawuyacin hali a jihar Nasarawa sun amfana daga shirin Household Prosperity and Empowerment (HOPE), wato shirin ƙarfafa gidaje da rage talauci.
Mai kula da shirin HOPE a jihar, Rhoda Agbawu, ce ta bayyana haka a yayin taron kwana ɗaya da aka gudanar a Lafia domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda shirin yake tafiya.
Ta ce taron ya samu halartar hukumomi daban-daban, kungiyoyin farar hula da na addinai domin tabbatar da shirin ya ci gaba da dorewa.
“Mun yi wannan taro ne domin tabbatar da shigar kowa cikin aikin aiwatar da shirin. Za mu haɗa kai da hukumar saka jari ta jihar Nasarawa domin tabbatar da cewa wannan shiri ya dore,” in ji ta.
Ta kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙirƙirar shirin tare da yin godiya ga Gwamna Abdullahi Sule bisa nuna kulawa da marasa galihu a jihar.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Tallafin Jama’a ta jihar Nasarawa (NSSIA), Malam Imran Jibrin, wanda shi ne mai magana sa yawun HOPE a jihar, ya ce shirin na da nufi shafar gidaje miliyan 15 da ke cikin talauci a faɗin ƙasar nan ta hanyar bai wa mutane kuɗi kai tsaye.
Ya ce a halin yanzu sama da gidaje miliyan biyu ne suka amfana a duk fadin Najeriya, inda aka kashe fiye da Naira biliyan 300.
“Gidaje da a da suke fama da ƙalubalen rayuwa yanzu sun samu sauƙi. Mata na iya ciyar da ’ya’yansu cikin kwanciyar hankali, gidaje kuma suna samun tallafi. Wannan ya dawo da martaba da fata mai kyau a zukatan mutane,” in ji Jibrin.
Ya ƙara da cewa tun daga 2021, gwamnatin jihar ta yi amfani da shirin tura kudi kai tsaye na conditional cash transfer wajen tallafa wa gidaje fiye da 10,000 a cikin ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Ita ma Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma ta jihar, Hajiya Hauwa Jugbo, ta gode wa Tinubu da Gwamna Sule bisa jajircewa wajen tallafa wa marasa galihu.
No comments