Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Ƙiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Ƙiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ya yarda da hukuncin korar da jam'iyyar NNPP ta yi masa, amma ya jaddada cewa yana nan kan bakar sa ta maganganun da ya yi a wata hira da wata kafar yaɗa Labarai.
Amma ya bayyana cewa, bai kamata Jam’iyyar ta yanke masa hukunci akan wani abu da ya faɗa ba, kamata ya yi Jam’iyyar ta kafa Kwamiti da zai saurari dalilin sa, ya kuma kare kansa akan maganganun da ya yi.
Hon. Kofa ya ce, amma maimakon haka, sai Jam’iyyar ta yanke shawarar korar sa daga Jam’iyyar gaba ɗaya wanda ba haka ya kamata ba.
Ya kara da cewa amma duk da haka ya amince da Matakin Jam’iyyar na Korar sa kuma babu wata damuwa akan matakin da aka dauka.
Ya ce jam'iyyar NNPP ta taimaka masa kuma shima ya taimaka mata sun taimaki juna a harkar Siyasa.
Hon. Abdlmumin Jibrin Kofa ya ce kuɗin da Jam’iyyar ke cewa ba ya biya, yana kira ga Shugabancin Jam’iyyar da su tura masa dukkan bayanai na ajiyar kuɗin jam'iyyar, kuma a shirye yake ya tura dukkan kuɗaɗen da ake magana a kai
Daga nan ya yi kira ga magoya bayan sa da su taho sabuwar tafiyar da za su shiga, amma duk wanda yake ganin zai ci gaba da tafiya a Jam’iyyar NNPP, ba shi da damuwa a hakan,
domin akwai mutuntaka a tsakani, kuma za su ci gaba da zumunci da juna, ba tare da cin mutuncin juna ba.
No comments