Gwamna Umaru Bago ya fayyace dokar da gwamnati ta bullo da ita domin daidaita harkokin wa’azi a jihar Neja. Ya ce, gwamnati ba ta haramta wa...
Gwamna Umaru Bago ya fayyace dokar da gwamnati ta bullo da ita domin daidaita harkokin wa’azi a jihar Neja.
Ya ce, gwamnati ba ta haramta wa’azi gaba ɗaya ba, sai dai ta yi dokar cewa Malaman addini su rinƙa gabatar da huɗubar su kafin su yi amfani da ita a masallatai ko coci.
Gwamna Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a shirin 'Siyasa a ranar Lahadi,' na gidan talabijin ɗin TVC a Abuja.
Gwamnan ya ce, “Ba mu hana wa’azi gaba ɗaya ba. Amma duk wanda zai yi huɗuba ranar Juma’a ko Lahadi, to sai ya kawo mana mun duba, mun tantance.
"Wannan abu ne na yau da kullum. Ko a Saudiyya haka ake yi. Ba za mu bar wani ya yi wa’azin da zai yi adawa da jama’a ko gwamnati ba."
Gwamnan ya bayyana cewa wannan tsari yana da nasaba da tsaro da kare jama’a daga kalaman da ka iya tayar da fitina. Akwai haɗin gwiwar DSS, ’yan sanda, NSCDC da sojoji.
Daraktan kula da harkokin addini na jihar Neja, Umar Farooq, ya ce dole ne duk wani Malami da ke son yin wa'azi ya samu lasisi a cikin watanni biyu.
Umar Farooq ya ce Malamai za su cike fom sannan kwamiti na musamman da aka kafa zai tantance su kafin a ba su lasisin yin wa'azi.
"Eh da gaske ne, gwamnatin jihar ta haramta yin wa'azi. Duk Malamin da ke son ya yi wa'azi zai nemi lasisi daga nan zuwa watanni biyu masu zuwa.
"Abin da kawai suke buƙata shi ne, su zo ofishin mu, su cike fom. Bayan nan, za su bayyana gaban kwamitin da zai tantance su, kafin su fara wa'azi," Umar Farooq.
Gwamna Umaru Gabo ya ce dokar ba da lasisin wa'azi a Neja za ta daƙile wa'azin da zai haifar da tashin hankali a jihar.
Babban Limamin Jami’a na jami'ar FUT da ke Minna, Bashir Yankuzo, ya ce wa’azi ibada ce kuma gwamnati ba ta da hurumin hana wa’azi.
Sai dai ya amince cewa gwamnati na iya sa baki idan aka yi amfani da wa’azi wajen tayar da hankalin jama’a.
Sakataren CAN reshen Neja, Raphael Opawoye, ya ce ba a sanar da su matakin gwamnatin ba tukuna, amma za su fito da matsayin su idan aka yi hakan.
Sai dai wani Malamin addini, Uthman Siraja, ya ce wannan mataki kutse ne ga ‘yancin addini, inda ya ba da shawarar a hukunta Malaman da suka saba ƙa'idojin wa'azi maimakon hana wa’azi gaba ɗaya.
No comments