Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Ma'aikatan NEMA Sun Ceto Wasu Mutane Daga Ambaliyar Ruwa A Kaduna

Ma'aikatan Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da ke Kaduna sun samu nasarar ceto wasu dattawa, waɗanda gini ya rufta masu saka...


Ma'aikatan Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da ke Kaduna sun samu nasarar ceto wasu dattawa, waɗanda gini ya rufta masu sakamakon wata ambaliyar ruwa da aka samu a jihar Kaduna.

Wannan aikin ceto ya gudana ne tare da haɗin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna (KADSEMA), hukumar taimakon gaggawa ta Red Cross, jami'an kashe gobata da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ceto, inda suka ceto wani dattijo a Bashama Road da ke Tudun wada Kaduna, da kuma wata dattijuwa a Kigo Road, wacce tuni aka miƙa ta ga 'yan uwan ta a Kabala Costain.

Hukumar ta ce tun a ranar Alhamis da ta gabata ne aka rinƙa samun wani mamakon ruwan sama a garin na Kaduna , wanda ya yi sanadiyyar korar wasu jama'a daga muhallan su, tare da asarar dukiya mai yawan gaske.

Ta ce, waɗanda wannan abin ya fi shafa, su ne waɗanda ke maƙwabtaka da Kogin Kaduna, wato Unguwannin Kigo Road, Bashama Road a Tudun Wada, Kinkinau, Malali, Ramat Road Rafin Guza da dai sauran su.

Hukumar ta ce ta ziyarci wuraren da waɗanda gidajen su suka ruguje har inda suke tsugune, inda ta tallafa masu da agajin katifu, barguna da gidan sauro.





 

No comments