Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan kiwon lafiya na mata masu juna biyu da jarirai kyauta, wanda darajar su ta kai Naira Biliyan 2.9 a faɗ...

An ƙaddamar da shirin ne a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, inda babban Daraktan hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (NPHCDA), Dakta Muyi Aina, ya ce wannan mataki wani bangare ne na ƙudirin gwamnati na samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mata da ƙananan yara, a ƙoƙarin rage mace-macen mata masu juna biyu a ƙasar.
Ya ce za a fara rabon ne a jihohi goma da suka fi fama da mace-mace a lokacin haihuwa, tare da kai kayan zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
“Shirin ya yi daidai da ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, wacce ta mayar da hankali wajen kare rayukan mata da yara,” in ji shi.
A cewar sa, an ware kashi 60 cikin 100 na kayan zuwa yankin Arewa maso Yamma, kashi 34 zuwa Arewa maso Gabas, yayin da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas suka raba sauran kaso.
Ya ƙara da cewa, shirin bai tsaya a kan raba kayayyaki kawai ba, domin za a inganta cibiyoyin kiwon lafiya, da horar da ma’aikata da kuma ƙara kayan aiki.
Haka zalika, wakiliyar ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO), Dakta Mary Brantwo, ta tabbatar da goyon bayan su ga Nijeriya, tare da cewa daga yanzu za a rika bin diddigin alƙaluman mace-macen mata a kowace shekara domin a ga yadda ake samun ci gaba.
Ƙungiyar UNICEF, UNFPA da kuma gidauniyar Gates su ma sun yaba da matakin gwamnatin, tare da shan alwashin ci gaba da bada goyon baya.
Kayayyakin da aka fara raba wa sun haɗa da kayan da ake buƙata yayin haihuwa “delivery packs”, magungunan jinya ga mata masu juna biyu, abubuwan ƙarin gina jiki, sanke mai maganin sauro da kuma muhimman magunguna ga mata da jarirai.
No comments