Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Aka Ƙayata Harabar Kabarin Marigayi Muhammadu Buhari

Al'umma da dama daga sassan ƙasar ƙasar nan suna ci gaba da ziyartar garin Daura ta jihar Katsina domin yi wa Marigayi Tsohon Shugaban ƙ...


Al'umma da dama daga sassan ƙasar ƙasar nan suna ci gaba da ziyartar garin Daura ta jihar Katsina domin yi wa Marigayi Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari addu'a, inda kuma yanzu haka an yi wa harabar kabarin gyara na musamman don mutunta shi.

An zagaye harabar ƙabarin da wani ƙarfe mai daraja, sannan an gina wata Hasumiya a mashigar harabar, an ƙyawata cikin harabar da wani irin dutse mai ɗaukar idanu.

Gwamnan Jihar Katsina, Dr Dikko Umar Raɗɗa yana daga cikin waɗanda suka kai wannan ziyara a 'yan kwanakin nan, inda ya jagoranci wata tawaga ta gwamnatin jihar, waɗanda suka haɗa da manyan jami’an gwamnatin.

A wannan ziyarar, Gwamna Raɗɗa da tawagar sa sun yi wa marigayin addu’ar nema masa rahamar Allah, tare da nema masa gafara.

Jama'a da dama na bayyana cewa wannan ziyara ta nuna irin alaƙa ta mutunci da girmamawa ga marigayin da Gwamnan ke da ita.





 

No comments