Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya NRC ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye da duk wasu gyare-gyare, inda ta ce a cik...
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Nijeriya NRC ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye da duk wasu gyare-gyare, inda ta ce a cikin mako mai zuwa, jiragen da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna za su dawo aiki gadangadan.
Wannan ya zo ne sakamakon samun nasarar kammala duk wasu gayre-gyare, tare da ɗaukar matakai na tsaro a wannan hanya.
In dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Agustan da ya gabata ne aka samu haɗarin zamewa daga kan dogo, wanda jirgin ya yi, wanda ta sanya dole aka dakatar da jigilar.
Shugaban sashen hulɗa da jama'a na Hukumar, Callistus Unyimadu ne ya tabbatar da wannan ci gaban, duk da dai bai bayyana takamaimar ranar da za a dawo da jigilar ba.
Mr Callistus ya bayyana cewa Hukumar ta yi namijin ƙoƙari wajen ganin an inganta gyaran Dogo, taragwai da sauran su, gyaran da ya zo daidai da zamani.
Haka Kakakin Hukumar ya bayyana cewa sun mayar wa da duk fasinjojin da abin rutsa da su kuɗaɗen su na waccan tafiyar, inda yanzu haka, cikin mutum 583 da suka yanki tikitin, an mayar wa da mutum 512 kuɗaɗen su.
“Ba mu tsaya nan ba, yanzu haka muna ci gaba da biyan kuɗaɗen sauran da suka rage don tabbatar da cewa ba a tsallake kowa ba," in ji shi.
A ƙarshe ya tabbatar da cewa, nan ba da jimawa ba za a fitar da sabon tsarin jigilar.
No comments