Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa cewa akwai wata rashin jituwa a tsakanin Gwamnan Ji...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa cewa akwai wata rashin jituwa a tsakanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A ranar Litinin ne jaridar Daily Nigerian ta fitar da wani labari wanda ke zargin cewa gwamnan na Kano ya daina ɗaukar wayar uban gidansa, wato Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da ya tayar da ƙura a kafofin sada zumunta.
Sai dai a wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan Kano kan harkar sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, ya ce babu wata rashin jituwa tsakanin Abba da mai gidan nasa Kwankwaso.
“Wannan zargin ba gaskiya ba ne kuma karkatar da hankali ne sakamakon Gwamna Abba yana da ladabi da alaƙa mai kyau da Sanata Rabiu Kwankwaso, inda yake kallonsa a matsayin jagora a jam’iyya da kuma tafiyarsa ta siyasa. Duk wata magana ta ɓaraka a tsakaninsu ba wai batu ne kawai na zuzutawa ba, amma ya saɓa wa mu’amularsu ta aiki.”
“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu sosai wajen tabbatar da aƙidu da hangen nesa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Ya kuma himmatu wajen samar da haɗin kai a cikin jam’iyyar tare da yin aiki tare da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar, ciki kuwa har da Kwankwaso domin cimma burinmu,” in ji sanarwar.

No comments