Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Huriya Dauda Lawal Ta Ɗauki Nauyin Yi Wa Matan Zamfara Aiki Kyauta

  Daga Hussaini Yero, Gusau Uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriya Dauda Lawal, ta ɗauki nauyin tantancewa da yi wa mata ɗari masu ɗa...

 

Daga Hussaini Yero, Gusau

Uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriya Dauda Lawal, ta ɗauki nauyin tantancewa da yi wa mata ɗari masu ɗauke da cutar kansar nono tiyata kyauta a faɗin jihar ta Zamfara.

Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana hakan ne a Litinin ɗin nan da ta gabata yayin bikin tunawa da ranar cutar nono ta duniya ta 2024 a jihar.

A jawabin ta, Hajiya Huriya ta bayyana cewa, "Yau ce ranar yaƙi da kansar nono ta duniya, don haka muka bi sahu wajen tallafa wa Mata masu ɗauke da wannan cuta mai haɗari da ke jawo asarasr rayuka a Jihar mu.

"Tare da goyon bayan maigidana gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, an tantance majinyata 100 da suka kamu da cutar kansar nono, kuma za a yi musu aikin tiyata kyauta a jihar.

“Ina farin cikin sanar da cewa ofishina tare da goyon bayan mai gidana Gwamna Dauda Lawal, za mu kula da waɗanda aka yi wa aikin yadda ya kamata don samun lafiya mai ɗorewa a gare su.

"Akan haka muke kira ga waɗanda za a yi ma aikin da su bi dokar likitoci a lokacin jinyar don samun nasarar aikin da ɗorewar lafiyar su.

No comments