Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umurnin a saki duk ƙananan yaran nan da aka kama a lokaci da kuma bayan Zanga-Zangar tsadar rayu...
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umurnin a saki duk ƙananan yaran nan da aka kama a lokaci da kuma bayan Zanga-Zangar tsadar rayuwa da ta gudana a ƙasar nan a watannin baya.
Ministan harkokin watsa labarai da wayar da kai, Alhaji Muhammad Idis ne ya bayyana haka yau Litinin a fadar shugaban ƙasa ta Vila da ke Abuja.
Ministan ya ƙara haske da cewa Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umurnin a janye duk tuhume-tuhumen da ake yi wa waɗannan ƙananan yara.
Haka kuma shugaba Tinubu ya umurci ma'aikatar harkokin jin ƙai da kawar da Talauci, ta duba irin buƙatun rayuwa na waɗannan yara don a tallafa masu.
.jpeg)
No comments